Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 24

Luka 24:27-41

Help us?
Click on verse(s) to share them!
27Sa'annan da farko daga Musa da har zuwa dukan annabawa, Yesu ya fasara masu duka abubuwa da ke game da kansa a dukan littattafai.
28Da suka yi kusa da kauyen, inda suke tafiya, ko da yake Yesu ya yi kamar zai wuce su.
29Amma suka tilasta shi, cewa, “Ka zauna da mu, gama yamma ta yi kusa rana kuma ta kusa karewa.” Sai Yesu ya tafi ya zauna da su.
30Ya faru cewa, sa'adda ya zauna tare da su domin ya ci abinci, sai ya dauki gurasan, ya albarkace shi, ya kakkarya, sai ya ba su.
31Sa'annan idanunsu suka bude, da suka gane shi, sai ya bace daga garesu,
32Suka ce wa junansu, ashe zuciyarmu ba ta yi kuna a cikinmu ba, sa'adda yake magana da mu a hanya, sa'adda ya bude mana littattafai?”
33Suka tashi a wancan sa'a, sai suka koma Urushalima. Suka sami sha dayan nan tare, da wadanda suke tare da su,
34cewa, “Lalle ne Ubangiji ya tashi, ya kuma bayyana ga Siman.”
35Sai suka fadi abubuwan da suka faru a hanya, da yadda aka bayyana masu Yesu sa'adda ya kakkarya gurasa.
36Sa'adda suke fadin wadannan abubuwan, sai Yesu ya tsaya a sakaninsu, sai ya ce masu, “Salama a gareku.”
37Amma suka firgita suna cike da tsoro, suna tsammani sun ga fatalwa.
38Yesu ya ce masu, don me ku ke damuwa? Don me tambayoyi ke tasowa a zuciyarku?
39Duba hannayena da kafafuna, cewa nine da kaina. Taba ni ku gani. Gama ruhu ba shi da jiki da kashi, kamar yadda ku ka ga nake da su.”
40Bayan da ya fadi wannan, sai ya nuna masu hannayensa da kafafunsa.
41Sa'adda suke cike da farin ciki, da mamaki, Yesu ya ce masu, “Kuna da wani abinci?”

Read Luka 24Luka 24
Compare Luka 24:27-41Luka 24:27-41