Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 1

Luka 1:49-72

Help us?
Click on verse(s) to share them!
49Domin shi madaukaki ya yi mani manyan abubuwa, kuma sunansa Mai Tsarki ne.
50Jinkansa ya tabbata daga tsara zuwa tsara wadanda suke girmama shi.
51Ya nuna karfinsa da hannuwansa; ya warwatsa ma su girman kai game da tunanin zuciyarsu.
52Ya nakasar da magada daga kursiyoyinsu, ya kuma fifita nakasassu.
53Ya ciyar da mayunwata da abubuwa masu kyau, amma ya aiki attajirai wofi.
54Ya ba da taimako ga bawan sa Isra'ila, domin ya tuna ya kuma nuna jinkai
55(kamar yanda ya fada wa ubaninmu) ga Ibrahim da zuriyarsa har abada.”
56Maryamu ta zauna da Alisabatu tsawon watanni uku sai ta koma gidanta.
57Da lokaci yayi da Alisabatu za ta haifi danta, ta kuma haifi da namiji.
58Makwabtanta da 'yan'uwanta sun ji cewa Ubangiji ya ribanbanya jinkansa akanta, sai suka yi murna tare da ita
59Ya zama akan rana ta takwas, sun zo domin a yi wa yaron kaciya. Da sun kira sunansa “Zakariya” kamar sunan ubansa,
60amma mahaifiyarsa ta amsa ta ce, “A'a, za a kira shi Yahaya.”
61Suka ce mata, “Babu wani a cikin danginku wanda ake kira da wannan suna.”
62Sun nuna alama ga ubansa bisa ga yanda ya ke so a rada masa suna.
63Ubansa ya nemi a ba shi allon rubutu, sai ya rubuta, “Sunansa Yahaya.” Dukan su suka yi mamaki kwarai da wannan.
64Nan take, sai bakinsa ya bude kuma harshensa ya saki. Ya yi magana ya kuma yabi Allah.
65Tsoro ya kama dukan wadanda suke zama kewaye da su. Sai labarin ya bazu cikin dukan kasar duwatsu ta Yahudiya.
66Kuma dukan wadanda suka ji su, sun ajiye su a cikin zuciyarsu, suna cewa, “To me wannan yaro zai zama ne?” Domin hannun Ubangiji yana nan tare da shi.
67Ruhu Mai-tsarki ya cika mahaifinsa Zakariya sai ya yi anabci cewa,
68“Yabo ga Ubangiji, Allah na Isra'ila domin ya zo ya taimaki mutanen sa kuma ya yi aikin ceto domin su.”
69Ya ta da kahon ceto dominmu daga gidan bawansa Dauda, daga zuriyar Dauda bawansa,
70kamar yadda ya fada ta bakin annabawansa tsarkaka tun zamanin zamanai.
71Zai kawo mana ceto daga magabtan mu da kuma daga hannun makiyanmu.
72Zai yi haka domin ya nuna jinkai ga ubaninmu ya kuma tuna da alkawarinsa mai tsarki,

Read Luka 1Luka 1
Compare Luka 1:49-72Luka 1:49-72