Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 14

Luka 14:9-16

Help us?
Click on verse(s) to share them!
9Sa'adda wanda ya gayyace ku duka biyu ya zo, zai ce maka, 'Ka ba mutumin nan wurinka,' sa'annan a kunyace za ka koma mazauni mafi kaskanci.
10Amma idan an gayyace ka biki, sai ka je ka zauna a wuri mafi kaskanci, domin idan wanda ya gayyace ka ya zo, yana iya ce maka, 'Aboki, hawo nan mana'. Sannan za ka sami girma kenan a gaban dukan wadanda kuke zaune tare a kan teburi.
11Duk wanda ya daukaka kansa, za a kaskantar da shi, wanda ya kaskantar da kansa, kuma daukaka shi za a yi”.
12Yesu ya ce wa mutumin da ya gayyace shi, “Idan za ka gayyaci mutum cin abinci ko biki, kada ka gayyaci abokanka, ko 'yan'uwanka, ko danginka, ko makwabtanka masu arziki, kamar yadda suna iya gayyatar ka, sai ya zama an maida maka.
13Amma idan za ka kira biki sai ka gayyace matalauta, da nakasassu, da guragu, da makafi,
14za ka kuwa sami albarka da yake ba su da hanyar saka maka. Gama za a saka maka a ranar tashin masu adalci.”
15Da daya daga cikin wadanda ke zama akan teburi da Yesu ya ji wadannan abubuwa, sai ya ce masa, “Albarka ta tabbata ga wanda zai ci abinci a mulkin Allah!”
16Amma Yesu ya ce masa, “Wani mutum ne ya shirya babban biki ya gayyaci mutane da yawa.

Read Luka 14Luka 14
Compare Luka 14:9-16Luka 14:9-16