Text copied!
Bibles in Hausa

Luka 14:9-16 in Hausa

Help us?

Luka 14:9-16 in Litafi Mai-tsarki

9 Sa'adda wanda ya gayyace ku duka biyu ya zo, zai ce maka, 'Ka ba mutumin nan wurinka,' sa'annan a kunyace za ka koma mazauni mafi kaskanci.
10 Amma idan an gayyace ka biki, sai ka je ka zauna a wuri mafi kaskanci, domin idan wanda ya gayyace ka ya zo, yana iya ce maka, 'Aboki, hawo nan mana'. Sannan za ka sami girma kenan a gaban dukan wadanda kuke zaune tare a kan teburi.
11 Duk wanda ya daukaka kansa, za a kaskantar da shi, wanda ya kaskantar da kansa, kuma daukaka shi za a yi”.
12 Yesu ya ce wa mutumin da ya gayyace shi, “Idan za ka gayyaci mutum cin abinci ko biki, kada ka gayyaci abokanka, ko 'yan'uwanka, ko danginka, ko makwabtanka masu arziki, kamar yadda suna iya gayyatar ka, sai ya zama an maida maka.
13 Amma idan za ka kira biki sai ka gayyace matalauta, da nakasassu, da guragu, da makafi,
14 za ka kuwa sami albarka da yake ba su da hanyar saka maka. Gama za a saka maka a ranar tashin masu adalci.”
15 Da daya daga cikin wadanda ke zama akan teburi da Yesu ya ji wadannan abubuwa, sai ya ce masa, “Albarka ta tabbata ga wanda zai ci abinci a mulkin Allah!”
16 Amma Yesu ya ce masa, “Wani mutum ne ya shirya babban biki ya gayyaci mutane da yawa.
Luka 14 in Litafi Mai-tsarki