Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 12

Luka 12:4-21

Help us?
Click on verse(s) to share them!
4Ina gaya maku abokaina, kada ku ji tsoron wanda da za su kashe jiki. Bayan haka kuma ba abin da za su iya yi.
5Bari in gargade ku a kan wanda za ku ji tsoronsa. Ku ji tsoron shi wanda bayan ya kashe zai iya jefa ku cikin jahannama. I, ina ce maku ku ji tsoronsa.
6Ba a kan sayar da 'yan tsuntsaye biyar a kan anini biyu ba? Duk da haka, Allah ba zai manta da ko daya daga cikinsu ba.
7Har ma gashin da ke kan ku ya san yawan su. Kada ku ji tsoro, ku kun fi tsuntsaye daraja a wurinsa.
8Ina gaya maku, dukan wanda za ya shaida ni a gaban mutane, Dan Mutum kuma za ya shaida shi a gaban mala'kun Allah.
9Kuma dukan wanda ya ki ni a gaban mutane, za a ki shi a gaban mala'ikun Allah.
10Dukan wanda ya yi magana gaba da Dan Mutum, za a gafarta masa. Amma shi wanda ya yi sabon Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba.
11Idan suka kawo ku gaban majami'a, ko gaban masu shari'a, ko gaban masu iko, kada ku damu da abin da za ku fada domin ku kare kanku. Ko kuwa abin da za ku ce.
12Gama Ruhu Mai Tsarki zai koya maku abin da za ku fadi a wannan lokaci.”
13Sai wani a cikin taron ya ce masa, “Malam, ka yi wa dan'uwana magana ya raba gado da ni
14Yesu ya ce masa, “Kai, wanene ya sa ni in zama alkali, ko matsakanci a kanku?”
15Sai kuma ya ce masu, “Ku yi lura kada ku zama masu hadama, gama ba abin da mutum ya mallaka ne ya fi mahimmanci a cikin rayuwar sa ba.”
16Sa'annan Yesu ya fada masu wani misali, ya ce, “Gonar wani mutum ta bada amfani sosai,
17ya yi tunani, ya ce, 'Me zan yi, domin ba ni da wurin da zan iya ajjiye amfanin gonata?'
18Sai ya ce, na san abin da zan yi. Zan rushe rumbuna na in gina wadansu manya-manya, a nan zan ajjiye hatsi na da dukan abubuwa.
19Sai in ce da raina, “Ya raina, kana da abu da yawa da aka ajjiye dominka, sai ka huta, ka ci, ka sha, ka yi murna.”
20Amma sai Allah ya ce da shi, 'Wawan mutum, a cikin daren nan ana son ranka daga wurinka. Kayan da ka tara ka shirya wa kanka, na wa za su zama?'
21Haka wanda ya tara wa kansa dukiya yake, idan ba shi da dukiya a wurin Allah.”

Read Luka 12Luka 12
Compare Luka 12:4-21Luka 12:4-21