Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 11

Luka 11:10-27

Help us?
Click on verse(s) to share them!
10Domin dukan wanda yake roko ya na karba; dukan wanda ya ke nema kuma yana samu; kuma wanda yake kwankwasawa, za a bude masa.
11Wanne uba ne a cikinku, idan dansa ya tambaye shi kifi, zai ba shi maciji a maimakon kifi?
12Ko kuwa idan ya tambaye shi kwai, za ya ba shi kunama?
13To, da yake ku da kuke masu mugunta kun san ku ba 'yanyan ku abu mai kyau. Yaya fa ga Ubanku wanda yake cikin sama, za ya ba da Ruhu Mai Tsarki ga wadanda suka roke shi?”
14Wani lokaci, Yesu yana fitar da wani beben aljani. Sa'adda aljanin ya fita, sai mutumin da yake bebe ya yi magana. Sai taron mutanen suka yi mamaki!
15Amma, wadansu daga cikin mutanen suka ce, “Da ikon Ba'alzabuba sarkin aljanu ne yake fitar da aljanu.”
16Wadansu suka gwada shi, suka nemi ya nuna masu wata alama daga sama.
17Amma Yesu da yake ya san tunaninsu, ya ce da su, “Dukan mulkin da ya rabu biyu, gaba da kansa, ya rushe kenan, kuma idan gida ya rabu biyu, gaba da kansa za ya fadi.
18Idan Shaidan ya rabu biyu gaba da kansa, ta yaya mulkinsa zai iya tsayawa? Gama kun ce ina fitar da aljanu ta wurin Ba'alzabuba.
19Idan ni na fitar da aljanu ta wurin Ba'alzabuba, ta wurin wa wadanda suke bin ku suke fitar da aljanu? Saboda haka, su ne zasu zama masu yi maku shari'a.
20Amma idan daga wurin Allah na ke fitar da aljanu, to, ya zama ke nan mulkin Allah ya zo wurinku.
21Idan mutum mai karfi, mai kayan fada ya tsare gidansa, kayansa za su tsira.
22Amma idan wani mutum wanda ya fi shi karfi ya zo ya ci nasara a kansa, zai dauke kayan fadan daga wurin mutumin, kuma ya kwashe kayansa.
23Wanda ba ya tare da ni, gaba da ni ya ke yi, kuma wanda ba ya tattarawa tare da ni, watsarwa yake yi.
24Idan kazamin ruhu ya fita daga cikin mutum, ya kan bi ta wurin busassun wurare yana neman wurin da zai huta. Idan bai samu ba sai ya ce, 'Bari in koma gidana inda na baro.
25Sa'adda ya dawo, ya tarar an share gidan, an kuma gyara shi tsaf.
26Sai ya je ya dauko wadansu aljanu guda bakwai wadanda su ka fi shi mugunta, su zo su zauna a wurin. Sai karshen mutumin nan ya fi farkonsa muni.”
27Ya zama, lokacin da ya ke fadin wadannan abubuwa, wata mace ta tada muryarta a cikin taron mutanen ta ce da shi, “Mai albarka ne cikin da ya haife ka, da maman da ka sha.”

Read Luka 11Luka 11
Compare Luka 11:10-27Luka 11:10-27