Text copied!
Bibles in Hausa

Luka 11:10-27 in Hausa

Help us?

Luka 11:10-27 in Litafi Mai-tsarki

10 Domin dukan wanda yake roko ya na karba; dukan wanda ya ke nema kuma yana samu; kuma wanda yake kwankwasawa, za a bude masa.
11 Wanne uba ne a cikinku, idan dansa ya tambaye shi kifi, zai ba shi maciji a maimakon kifi?
12 Ko kuwa idan ya tambaye shi kwai, za ya ba shi kunama?
13 To, da yake ku da kuke masu mugunta kun san ku ba 'yanyan ku abu mai kyau. Yaya fa ga Ubanku wanda yake cikin sama, za ya ba da Ruhu Mai Tsarki ga wadanda suka roke shi?”
14 Wani lokaci, Yesu yana fitar da wani beben aljani. Sa'adda aljanin ya fita, sai mutumin da yake bebe ya yi magana. Sai taron mutanen suka yi mamaki!
15 Amma, wadansu daga cikin mutanen suka ce, “Da ikon Ba'alzabuba sarkin aljanu ne yake fitar da aljanu.”
16 Wadansu suka gwada shi, suka nemi ya nuna masu wata alama daga sama.
17 Amma Yesu da yake ya san tunaninsu, ya ce da su, “Dukan mulkin da ya rabu biyu, gaba da kansa, ya rushe kenan, kuma idan gida ya rabu biyu, gaba da kansa za ya fadi.
18 Idan Shaidan ya rabu biyu gaba da kansa, ta yaya mulkinsa zai iya tsayawa? Gama kun ce ina fitar da aljanu ta wurin Ba'alzabuba.
19 Idan ni na fitar da aljanu ta wurin Ba'alzabuba, ta wurin wa wadanda suke bin ku suke fitar da aljanu? Saboda haka, su ne zasu zama masu yi maku shari'a.
20 Amma idan daga wurin Allah na ke fitar da aljanu, to, ya zama ke nan mulkin Allah ya zo wurinku.
21 Idan mutum mai karfi, mai kayan fada ya tsare gidansa, kayansa za su tsira.
22 Amma idan wani mutum wanda ya fi shi karfi ya zo ya ci nasara a kansa, zai dauke kayan fadan daga wurin mutumin, kuma ya kwashe kayansa.
23 Wanda ba ya tare da ni, gaba da ni ya ke yi, kuma wanda ba ya tattarawa tare da ni, watsarwa yake yi.
24 Idan kazamin ruhu ya fita daga cikin mutum, ya kan bi ta wurin busassun wurare yana neman wurin da zai huta. Idan bai samu ba sai ya ce, 'Bari in koma gidana inda na baro.
25 Sa'adda ya dawo, ya tarar an share gidan, an kuma gyara shi tsaf.
26 Sai ya je ya dauko wadansu aljanu guda bakwai wadanda su ka fi shi mugunta, su zo su zauna a wurin. Sai karshen mutumin nan ya fi farkonsa muni.”
27 Ya zama, lokacin da ya ke fadin wadannan abubuwa, wata mace ta tada muryarta a cikin taron mutanen ta ce da shi, “Mai albarka ne cikin da ya haife ka, da maman da ka sha.”
Luka 11 in Litafi Mai-tsarki