Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 4

Ayyukan Manzanni 4:8-21

Help us?
Click on verse(s) to share them!
8Sai Bitrus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya ce, “Ku shugabanni da dattawan jama'a,
9idan mu yau ana tuhumarmu saboda aikin kirki da aka yi ga wannan mara lafiya - ta yaya wannan mutum ya sami lafiya?
10Bari ku da dukan mutanen Isra'ila, ku san wannan, cikin sunan Yesu Almasihu Banazare, wanda kuka giciye, wanda Allah ya tayar daga matattu ta dalilinsa ne wannan mutumin yake tsaye a gaban ku lafiyayye.
11Yesu Almasihu ne dutsen da ku magina kuka ki, amma an mai da shi kan gini.
12Babu ceto daga kowanne mutum, domin babu wani suna da aka bayar karkashin sama, a cikin mutane wanda ta wurinsa za a iya samu ceto.”
13Sa'adda, suka ga karfin halin Bitrus da Yahaya, suka gane mutane ne talakawa marasa ilimi, sai suka yi mamaki, suka kuma lura suka gane Bitrus da Yahaya sun kasance tare da Yesu.
14Da yake suna ganin mutumin nan da aka warkar tare da su, sai suka rasa abin yi.
15Amma bayan sun fitar da manzannin daga majalisa sai suka tattauna a tsakaninsu.
16Suka ce, “Yaya za mu yi da wadannan mutane? Babu shakka aikin al'ajibi ya faru ta wurinsu, kuma sananne ne ga dukan mazauna Urushalima, kuma ba mu da iko mu musanci haka.
17Amma saboda kada ya cigaba da yaduwa cikin mutane, bari mu yi masu kashedi kada su kara magana da kowa cikin wannan suna.”
18Suka kira Bitrus da Yahaya suka dokace su kada su kara magana ko kuma koyarwa ko kadan a cikin sunan Yesu.
19Amma Bitrus da Yahaya suka amsa suka ce, “Ko ya yi daidai a gaban Allah mu yi maku biyayya fiye da shi, ku hukunta.
20Baza mu iya daina magana game da abubuwan da muka ji kuma muka gani ba.”
21Bayan sun sake yi wa Bitrus da yahaya kashedi, sai suka sake su, su tafi. Domin ba su iya samu wata hujja da za su hore su a kai ba, domin dukan mutane suna yabon Allah saboda abin da ya faru.

Read Ayyukan Manzanni 4Ayyukan Manzanni 4
Compare Ayyukan Manzanni 4:8-21Ayyukan Manzanni 4:8-21