Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 28

Ayyukan Manzanni 28:20-26

Help us?
Click on verse(s) to share them!
20Saboda wannan ne na bukaci ganinku in yi magana da ku. Saboda begen da Isra'ila suke da shi ya sa nake daure da wannan sarkar”.
21Sai suka ce masa, “Bamu karbi wasiku daga Yahudiya game da kai ba, babu kuma wani daga cikin 'yan'uwa wanda ya kawo mana wani rahoto ko wata magana game da kai.
22Amma muna so mu ji daga gare ka abin da kayi tunani ka kuma gani game da wannan darikar, gama mun sani ana kushenta a ko'ina.”
23Sa'adda suka sa masa rana, mutane da dama suka same shi a masaukinsa. Ya gabatarda zantattukan a gare su, yana tabbatar da bayyanuwar mulkin Allah. Har ya nemi ya rinjaye su a kan zancen Yesu, tun daga attaurat ta Musa zuwa litattafan annabawa, ya yi wannan tun daga safiya har yamma.
24Wasu sun kawar da shakkar abin da aka fada, amma wadansu basu gaskanta ba.
25Da shike ba su yarda da junansu ba, sai suka tafi bayan da Bulus ya fadi kalma daya, “Ruhu Mai Tsarki ya yi magana ta bakin annabi Ishaya zuwa ga kakanninku.
26Ya ce, 'Jeka wurin al'umman nan ka ce, cikin ji zaku ji amma ba zaku fahimta ba; zaku gani amma ba zaku gane ba.

Read Ayyukan Manzanni 28Ayyukan Manzanni 28
Compare Ayyukan Manzanni 28:20-26Ayyukan Manzanni 28:20-26