Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 9

Luka 9:16-37

Help us?
Click on verse(s) to share them!
16Ya dauki dunkulen gurasan guda biyar, da kifin guda biyu, yana dubawa zuwa sama ya albakarce su, sa'annan ya gutsuttsura, ya ba almajiran domin su rarraba wa mutane.
17Dukansu suka ci kowa ya koshi. Daga nan almajiran suka tattara sauran abin da ya rage, har kwanduna goma sha biyu suka cika!
18Wata rana Yesu yana yin addu'a shi kadai, sai almajiransa suka zo sai ya tambaye su, “Wa mutane suke cewa da ni?”
19Suka amsa, “Wadansu suna cewa, Yahaya mai yin Baftisma, wadansu suna cewa kai annabi Iliya ne, har yanzu wadansu suna cewa kai wani cikin annabawa na da can ne ya dawo da rai.”
20Ya tambaye su, “Ku fa? Wa kuke cewa da ni?” Bitrus ya amsa, “Kai Almasihu ne wanda ya zo daga wurin Allah.”
21Sai Yesu ya gargade su da karfi, kada su gayawa kowa haka tukuna.
22Sa'annan ya ce, “Dan Mutum dole ya sha wahalar abubuwa da yawa; dattawa za su ki shi da manyan fristoci da marubuta, sa'annan za a kashe shi. Bayan kwana uku, za a tashe shi da rai.”
23Sai ya ce da su duka, “Dukan wanda ya ke so ya biyo ni, dole ne ya yi musun kansa, ya dauki gicciyen sa kulluyomin, ya biyo ni.
24Dukan wanda yake so ya ceci ransa, za ya rasa shi, amma dukan wanda ya ba da ransa domina, za ya cece shi.
25Wacce riba mutum zai samu idan ya sami duniya duka, amma ya rasa ransa?
26Dukan wanda yake jin kunya ta da magana ta, Dan Mutum ma zai ji kunyarsa, sa'adda ya dawo cikin darajarsa da darajar Uba da ta mala'iku masu tsarki.
27Amma ina gaya maku wannan tabbas, wadansu cikinku da ke nan tsaye, ba za su mutu ba sai sun ga mulkin Allah.”
28Kwana takwas bayan Yesu ya fadi wadannan kalmomi, sai ya dauki Bitrus da Yahaya da Yakubu, ya hau kan dutse domin ya yi addu'a a can.
29Sa'anda ya ke yin addu'a sai yanayin fuskar sa ya canza sosai, tufafinsa kuma suka yi sheki da haske kamar walkiya.
30Nan da nan sai ga mutane biyu suna magana da shi, wato Musa da Iliya.
31Suka bayyana da daraja kewaye da su, suka yi magana da Yesu a kan tafiyarsa wadda za ta zo ba da dadewa ba a cikin Urushalima.
32Bitrus da almajiran da suke tare da shi barci mai nauyi ya dauke su. Sa'adda suka farka sai su suka ga daukakar Yesu; kuma suka ga mutanen su biyu da ke tsaye tare da shi.
33Sa'adda Musa da Iliya suke shirin su bar wurin Yesu, sai Bitrus ya ce, “Ya shugaba, ya yi kyau da muke a nan. Zai yi kyau mu yi runfuna uku, daya dominka, daya domin Musa, daya kuma domin Iliya.” Amma hakika bai san abin da ya ke fadi ba.
34Sa'adda yake fadin haka sai wani girgije ya zo ya rufe su. Sai suka ji tsoro sa'adda girgijen ya kewaye su.
35Sai ga wata murya daga cikin girgijen tana cewa, “Wannan Dana ne wanda na zaba, ku ji shi.”
36Sa'adda muryar ta gama magana, Yesu yana nan shi kadai. Suka yi shiru ba su iya cewa kome ba a kan abin da suka gani a kwanakin nan.
37Washe gari, da suka sauko daga kan dutsen, sai taron mutane da yawa suka zo wurinsa.

Read Luka 9Luka 9
Compare Luka 9:16-37Luka 9:16-37