1Idan akwai wani abin karfafawa cikin Almasihu. Idan da wata ta'aziyya daga kaunarsa. Idan akwai zumunta a Ruhu. Idan da tatausan jinkai da tausayi.
2Ku cika farin cikina don ku zama da tunani irin haka, kuna da kauna daya, kuna tarayya cikin Ruhu daya, ku kasance da manufa iri daya.
3Kada ku yi komai cikin sonkai ko girman kai. A maimakon haka cikin zuciya mai tawali'u kowa na duban wadansu fiye da kansa.
4Kada kowa ya dubi bukatun sa, amma yana lura da bukatun wadansu.
5Ku yi tunani cikin hanya wadda ke cikin Almasihu Yesu.
6Wanda ya yi zama cikin siffar Allah, bai mai da daidaitarsa da Allah wani abin da zai rike ba.
7Maimakon haka, ya wofintar da kansa. Ya dauki siffar bawa. Ya bayyana cikin kamannin mutane. An same shi a bayyane kamar mutum.
8Ya kaskantar da kansa, ya yi biyayya har ga mutuwa, mutuwa ta gicciye.
9Saboda haka Allah ya ba shi mafificiyar daukaka. Ya ba shi suna wanda yafi kowanne suna.
10Domin a cikin sunan Yesu kowace gwiwa za ta durkusa, gwiwoyin wadanda ke cikin sama da kuma duniya da kuma karkashin duniya.
11Kuma kowanne harshe zai furta cewa Yesu Almasihu Ubangiji ne, zuwa daukakar Allah Uba.
12Domin wannan kaunatattuna, kamar yadda kullum kuke biyayya ba sai ina nan kadai ba. Balle yanzu da bananan, ku yi aikin cetonku da tsoro da far gaba.
13Gama Allah ne yake aiki a cikinku ku yi nufi duka da aikata abin da zai gamshe shi.
14Ku yi kowanne abu ba tare da gunaguni da gardama ba.
15Domin ku zama marasa abin zargi kuma masu gaskiya, 'ya'yan Allah marasa aibi. Ku yi haka domin ku haskaka kamar haske a cikin wannan duniya, a tsakiyar karkatacciyar da gurbatacciyar tsara.