Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 4

Ayyukan Manzanni 4:1-17

Help us?
Click on verse(s) to share them!
1Yayin da Bitrus da Yahaya suna kan magana da mutanen, sai firistoci da shugaban masu tsaron Haikali da kuma Sadukiyawa suka afko masu.
2Sun damu sosai domin Bitrus da Yahaya suna koyar da mutane game da Yesu kuma suna shelar tashinsa daga matattu.
3Suka kama su suka jefa kurkuku sai washegari, domin yamma ta riga ta yi.
4Amma mutane da yawa da suka ji sakon suka ba da gaskiya; kimanin mazaje dubu biyar ne kuwa suka ba da gaskiya.
5Washegari, da shugabaninsu, da dattawansu, da Marubuta suka taru a Urushalima.
6Anas babban firist, yana nan, da Kayafa, da Yahaya da Iskandari, da dukan dangin babban firist
7Da suka kawo Bitrus da Yahaya a tsakiyarsu sai suka tambaye su, “Da wanne iko, ko cikin wanne suna k ka yi haka?”
8Sai Bitrus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya ce, “Ku shugabanni da dattawan jama'a,
9idan mu yau ana tuhumarmu saboda aikin kirki da aka yi ga wannan mara lafiya - ta yaya wannan mutum ya sami lafiya?
10Bari ku da dukan mutanen Isra'ila, ku san wannan, cikin sunan Yesu Almasihu Banazare, wanda kuka giciye, wanda Allah ya tayar daga matattu ta dalilinsa ne wannan mutumin yake tsaye a gaban ku lafiyayye.
11Yesu Almasihu ne dutsen da ku magina kuka ki, amma an mai da shi kan gini.
12Babu ceto daga kowanne mutum, domin babu wani suna da aka bayar karkashin sama, a cikin mutane wanda ta wurinsa za a iya samu ceto.”
13Sa'adda, suka ga karfin halin Bitrus da Yahaya, suka gane mutane ne talakawa marasa ilimi, sai suka yi mamaki, suka kuma lura suka gane Bitrus da Yahaya sun kasance tare da Yesu.
14Da yake suna ganin mutumin nan da aka warkar tare da su, sai suka rasa abin yi.
15Amma bayan sun fitar da manzannin daga majalisa sai suka tattauna a tsakaninsu.
16Suka ce, “Yaya za mu yi da wadannan mutane? Babu shakka aikin al'ajibi ya faru ta wurinsu, kuma sananne ne ga dukan mazauna Urushalima, kuma ba mu da iko mu musanci haka.
17Amma saboda kada ya cigaba da yaduwa cikin mutane, bari mu yi masu kashedi kada su kara magana da kowa cikin wannan suna.”

Read Ayyukan Manzanni 4Ayyukan Manzanni 4
Compare Ayyukan Manzanni 4:1-17Ayyukan Manzanni 4:1-17