Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Markus - Markus 7

Markus 7:14-33

Help us?
Click on verse(s) to share them!
14Ya kara kiran taron jama'ar yace masu, “ku kasa kunne gareni, kuma ku gane.
15Babu wani abu daga wajen mutum da zai iya gurbatar da shi har idan ya shiga cikinsa. Amma, abinda ya fita daga cikinsa shike gurbatar da shi”
16Bari mai kunnen ji, ya ji.
17Da Yesu ya bar taron jama'ar, ya shiga gida, sai almajiransa suka tambaye shi ma'anar wannan misali.
18Sai Yesu yace, 'ashe baku da ganewa? ko baku sani cewa abin da ya shiga cikin mutum daga waje ba zai iya gurbatar da shi ba,
19domin ba zai iya kai wa cikin zuciyarsa ba, sai dai ya shiga cikin sa ya kuma fita a matsayin bayan gari a salga”. Da wannan magana, Yesu ya mayar da dukan abinci ya zama da tsabta.
20Ya ce, abinda ke cikin mutum shike gurbatar da shi
21Domin daga cikin mutum, kuma daga cikin zuciyarsa ne, mugun tunani, lalata, sata, kisa,
22zina, kwadayi, mugunta, hai'inci, mugun guri, kishi, zargi, girmankai, wawanci.
23Duk wadannan miyagun abubuwa suna fitowa ne daga cikin mutum, kuma suke gurbatar da shi.”
24Ya tashi daga nan ya tafi shiyyar Sur da Sida. Ya shiga wani gida don baya son wani ya sani cewa yana nan, amma bai iya boyuwa ba.
25Amma nan da nan wata mace, wadda diyarta ke da mugun ruhu-wannan mace kuwa ta ji game da Yesu sai ta zo ta durkusa a gabansa.
26Matar yar kasar Girka ce, kuma asalinta daga Fonishiya take. Ta roke shi da ya fitar da mugun ruhun nan daga diyarta.
27Sai ya ce mata, “Bari a ciyar da 'ya'ya tukuna. Domin bai kamata a dauki abincin yaya a ba karnuka ba”.
28Sai ta amsa masa cewa, “I, Ubangiji, Karnukan ma sukan ci abincin da ke fadowa daga teburin 'ya'yan.”
29Ya ce mata, “domin kin fadi haka, kina iya ki tafi domin aljani ya fita daga diyarki.”
30Ta koma gida sai ta iske diyarta na kwance akan gado, aljanin ya fice daga jikinta.
31Ya sake fita daga shiyar Sur, ya biyo ta Sidon, har zuwa tekun Galili a shiyar Dikafolis.
32Sun kawo masa wani kurma, kuma bebe ne shi, suna rokansa ya dora hanuwansa a bisansa.
33Sai ya jawo shi daga taron jama'ar, zuwa gefe, sai ya sa hanunsa a kunuwan beben bayan ya tufa yawunsa, sannan ya taba harshensa.

Read Markus 7Markus 7
Compare Markus 7:14-33Markus 7:14-33