Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 1

Luka 1:20-63

Help us?
Click on verse(s) to share them!
20Kuma duba, za ka zama bebe, ba za ka iya magana ba, sai ran da wadannan abubuwa suka cika. Ya zama haka domin ba ka gaskanta da kalmomina ba, wadanda za su cika a daidai lokacin.”
21Sa'adda mutane suke jiran Zakariya. Sun yi mamaki yadda ya dauki lokaci sosai a cikin haikali.
22Amma da ya fita, bai iya yin magana da su ba. Sun gane da cewa ya ga wahayi lokacin da yake cikin haikali. Ya ci gaba da yi masu alamu, ba ya magana.
23Ya zama bayan da kwanakin hidimarsa suka kare, ya tafi gidansa.
24Bayan kwanakin nan, matarsa Alisabatu ta samu juna biyu. Ta boye kanta har na watani biyar. Ta ce,
25“Wannan shi ne abin da Allah ya yi mani da ya dube ni domin ya dauke kunyata a gaban jama'a.”
26A cikin watan ta na shidda, an aiki Mala'ika Jibra'ilu daga wurin Allah zuwa wani birni a Galili mai suna Nazarat,
27zuwa ga wata budurwa wanda aka ba da ita ga wani mutum mai suna Yusufu. Shi dan zuriyar Dauda ne, kuma ana kiran budurwar Maryamu.
28Ya zo wurin ta ya ce, “A gaishe ki, ke da ki ke da tagomashi sosai! Ubangiji yana tare da ke.
29Amma ta damu kwarai da wadannan kalmomi sai ta yi tunani ko wacce irin gaisuwa ce wannan.
30Mala'ikan ya ce mata, “Kada ki ji tsoro, Maryamu, domin kin samu tagomashi a wurin Allah.
31Duba, za ki sami juna biyu, za ki haifi da. Za ki kira sunansa 'Yesu'.
32Zai zama mai girma, kuma za a ce da shi Dan Allah Madaukaki. Ubangiji Allah zai ba shi kursiyin ubansa Dauda.
33Zai yi mulkin dukkan gidan Yakubu har abada, kuma mulkinsa ba shi da iyaka.”
34Maryamu ta ce wa mala'ikan, “Yaya wannan zai faru, tun da shike ni ban san namiji ba?”
35Mala'ikan ya amsa ya ce mata, “Ruhu Mai-tsarki zai sauko a kan ki, kuma ikon Madaukaki zai lullube ki. Sabili da haka, za a kira mai tsarkin da za ki haifa Dan Allah.
36Ki kuma duba, ga 'yar'uwarki Alisabatu ta samu juna biyu a tsufanta. Watannin ta shida kenan, ita wadda aka kira ta bakarariya.
37Gama babu abin da ba shi yiwuwa a wurin Allah.”
38Maryamu ta ce, “To, ni baiwar Ubangiji ce. Bari ya faru da ni bisa ga sakonka.” Sai mala'ikan ya bar ta.
39Sai Maryamu ta tashi da sauri a cikin kwanakin nan, zuwa kasa mai duwatsu, zuwa wani birni a Yahudiya.
40Ta shiga gidan Zakariya ta kuma gai da Alisabatu.
41Ya zama sa'adda Alisabatu ta ji gaisuwar Maryamu, sai dan da ke cikinta ya yi tsalle, an cika Alisabatu kuma da Ruhu Mai Tsarki.
42Ta daga murya, ta ce, “Mai albarka kike a cikin mata, kuma mai albarka ne dan cikinki.
43Kuma don me ya faru da ni da uwar Ubangijina ta ziyarce ni?
44Kuma duba, da na ji karar gaisuwan ki sai dan ciki na ya yi tsalle domin murna.
45Kuma mai albarka ce wadda ta gaskanta cewa abubuwan da aka alkawarta mata daga wurin Ubangiji za su cika.
46Maryamu ta ce, “Zuciyata ta yabi Ubangiji,
47kuma ruhu na ya yi murna da Allah mai ceto na.”
48Domin ya dubi kaskancin baiwarsa. Duba, daga yanzu, dukkan tsararraki za su ce da ni mai albarka.
49Domin shi madaukaki ya yi mani manyan abubuwa, kuma sunansa Mai Tsarki ne.
50Jinkansa ya tabbata daga tsara zuwa tsara wadanda suke girmama shi.
51Ya nuna karfinsa da hannuwansa; ya warwatsa ma su girman kai game da tunanin zuciyarsu.
52Ya nakasar da magada daga kursiyoyinsu, ya kuma fifita nakasassu.
53Ya ciyar da mayunwata da abubuwa masu kyau, amma ya aiki attajirai wofi.
54Ya ba da taimako ga bawan sa Isra'ila, domin ya tuna ya kuma nuna jinkai
55(kamar yanda ya fada wa ubaninmu) ga Ibrahim da zuriyarsa har abada.”
56Maryamu ta zauna da Alisabatu tsawon watanni uku sai ta koma gidanta.
57Da lokaci yayi da Alisabatu za ta haifi danta, ta kuma haifi da namiji.
58Makwabtanta da 'yan'uwanta sun ji cewa Ubangiji ya ribanbanya jinkansa akanta, sai suka yi murna tare da ita
59Ya zama akan rana ta takwas, sun zo domin a yi wa yaron kaciya. Da sun kira sunansa “Zakariya” kamar sunan ubansa,
60amma mahaifiyarsa ta amsa ta ce, “A'a, za a kira shi Yahaya.”
61Suka ce mata, “Babu wani a cikin danginku wanda ake kira da wannan suna.”
62Sun nuna alama ga ubansa bisa ga yanda ya ke so a rada masa suna.
63Ubansa ya nemi a ba shi allon rubutu, sai ya rubuta, “Sunansa Yahaya.” Dukan su suka yi mamaki kwarai da wannan.

Read Luka 1Luka 1
Compare Luka 1:20-63Luka 1:20-63