Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 1

Luka 1:1-13

Help us?
Click on verse(s) to share them!
1Mutane da dayawa sun yi kokarin rubutu akan abubuwan da suka cika a tsakaninmu,
2kamar yanda suka danka mana su, wadanda tun daga farko suka zama shaidu da idanunsu kuma manzanni ne na sakon.
3Sabili da haka, ni ma, bayan da na yi bincike da kyau akan yanayin wadannan abubuwa tun da farko na ga ya yi kyau in rubuta wadannan abubuwa bi da bi ya mafi girmaTiyofilas.
4Ya zama haka domin ka san gaskiyar abin da aka koya maka ne.
5A cikin zamanin Hirudus, Sarkin Yahudiya, akwai wani firist mai suna Zakariya, daga yankin Abija. Matarsa daga cikin yaya mata na zuriyar Haruna ce, kuma sunan ta Alisabatu ne.
6Dukan su biyu masu adalci ne a gaban Allah; marasa zargi a tafiyarsu cikin dukan dokoki da farilan Ubangiji.
7Amma ba su da da, domin Alisabatu ba ta haihuwa, kuma a wannan lokacin dukansu sun tsufa kwarai.
8Ya zama kuma a lokacin da Zakariya yana gaban Allah, yana yin hidimar sa ta firist bisa ga tsari da ka'idar aikinsa.
9Bisa ga al'adar zaben firist da zai yi hidima, an zabe shi ta wurin kuri'a ya shiga cikin haikalin Ubangiji domin ya kona turare.
10Dukan taron Jama'a suna addu'a a waje a sa'adda ake kona turaren.
11A lokacin, mala'ikan Ubangiji ya bayana a gare shi yana tsaye a gefen daman bagadi na turaren.
12Zakariya ya firgita sa'adda ya gan shi; tsoro ya kama shi.
13Amma mala'ikan ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, Zakariya, domin an ji addu'ar ka. Matar ka Alisabatu za ta haifa maka da. Za ka kira sunansa Yahaya.

Read Luka 1Luka 1
Compare Luka 1:1-13Luka 1:1-13