Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 16

Luka 16:16-23

Help us?
Click on verse(s) to share them!
16Attaura da litattafan annabawa suna nan har zuwan Yahaya. Tun daga lokacin nan ake yin bisharar mulkin Allah, kowa kuma yana kokarin kutsawa zuwa cikinta.
17Duk da haka, zai fi sauki sama da kasa su shude, da ko digo daya na attaura ya shude.
18Duk wanda ya saki matansa ya auri wata ya aikata zina, kuma wanda ma ya auri sakakkiya ya aikata zina.
19Akwai wani mai arziki, mai sa tufafi na alfarma masu tsada yana shagalin sa kowace rana.
20Aka ajiye wani gajiyayye a kofarsa, mai suna liazaru wanda duk jikinsa miki ne,
21Shi kuwa yana marmarin ya koshi da barbashin da ke fadowa daga teburin mai arzikin nan har ma karnuka sukan zo suna lasar mikinsa.
22Ana nan sai gajiyayyen nan ya mutu, malaiku kuma suka dauke shi suka kai shi wurin Ibrahim. Mai arzikin ma ya mutu, aka kuma binne shi,
23yana cikin hades yana shan azaba, sai ya daga kai ya hangi Ibrahim daga nesa, da Li'azaru a kirjinsa.

Read Luka 16Luka 16
Compare Luka 16:16-23Luka 16:16-23