Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 15

Luka 15:7-14

Help us?
Click on verse(s) to share them!
7Ina gaya maku, haka kuma za a yi farin ciki a sama, a kan mai zunubi guda da ya tuba, fiye da kan masu adalci tassa'in da tara wadanda ba su bukatar tuba.
8Ko kuwa wacce mace ce, in tana da kudi azurfa guda goma, in ta batar da daya, ba za ta kunna fitila ta share gidan, ta yi ta neman shi har sai ta same shi ba?
9In kuwa ta same shi sai ta tara kawayenta da makwabtanta, ta ce, 'Ku taya ni farin ciki don na sami kudin nan nawa da ya bace.'
10Haka nake gaya maku, abin farin ciki ne ga mala'ikun Allah idan mai zunubi guda ya tuba.”
11Sai Yesu ya ce, “Akwai wani mutum mai 'ya'ya biyu maza,
12sai karamin ya ce wa mahaifinsa, 'Baba, bani rabona daga cikin dukiyarka.' Sai mahaifinsa ya raba masu dukiyarsa tsakaninsu.
13Bayan 'yan kwanaki kadan, sai karamin dan ya tattara duk mallakarsa, ya kama hanya zuwa wata kasa mai nisa. A can ya batas da kudinsa, yana sayan abubuwan da ba ya bukata, ya kuma batas da kudinsa a wajen masha'a.
14Bayan da ya batas da duk abin da ya ke da shi, sai aka yi babbar yunwa a kasar, sai ya shiga fatara.

Read Luka 15Luka 15
Compare Luka 15:7-14Luka 15:7-14