Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya - Yahaya 5

Yahaya 5:31-47

Help us?
Click on verse(s) to share them!
31Idan zan yi shaida game da kaina, shaidata baza ta zama gaskiya ba.
32Akwai wani wanda ya ke bada shaida game da ni, na kuwa sani shaidar da yake bayarwa game da ni gaskiya ce.
33Kun aika zuwa wurin Yahaya, shi kuma ya yi shaidar gaskiya.
34Duk da haka shaidar da na karba bata mutum bace. Na fadi wadanan abubuwa domin ku sami ceto.
35Yahaya fitila ne mai ci, mai haske ne kuma, kun yarda ku yi farinciki da haskensa dan lokaci kadan.
36Amma shaidar da ni ke da ita ta fi ta Yahaya karfi. Domin ayyukan da Uba ya bani ni in yi, wato ainihin ayyukan da nake yi, su ne suke shaida ta cewa, Uba ne ya aiko ni.
37Uba wanda ya aiko ni, shi da kansa ya shaide ni. Ba ku taba jin muryar sa ba, ko ganin kamanninsa.
38Maganarsa kuwa ba ta zaune a zuciyarku, domin baku gaskata da wanda ya aiko ni ba.
39Kuna nazarin littattafai, don a tsammaninku a cikinsu za ku sami rai Madawwami, alhali kuwa su ne suke shaidata.
40kuma baku niyyar zuwa wurina domin ku sami rai.
41Ba na karbar yabo daga wurin mutane,
42amma na sani baku da kaunar Allah a zuciyarku.
43Na zo a cikin sunan Ubana, amma ba ku karbe ni ba. Idan wani ya zo da sunan kansa, za ku karbe shi.
44Ta yaya za ku ba da gaskiya, ku da kuke karban yabo daga junanku, amma ba ku neman yabon dake zuwa daga wurin Allah?
45Kada ku yi tunani zan zarge ku a wurin Uba. Mai zargin ku shine Musa, wanda kuka sa begenku a cikin sa.
46Inda kun gaskata Musa, da kun gaskata da ni domin ya yi rubutu game da ni.
47Idan kuwa ba ku gaskata abin da ya rubuta ba, ta yaya za ku gaskata maganata?”

Read Yahaya 5Yahaya 5
Compare Yahaya 5:31-47Yahaya 5:31-47