Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Romawa - Romawa 5

Romawa 5:3-11

Help us?
Click on verse(s) to share them!
3Ba kuwa haka kadai ba, amma muna murna da shan wahalolinmu. Mun san cewa shan wuya na haifar da
4Jimiri, Jimiri kuma na kawo amincewa, amincewa na kawo gabagadi game da abin da zai zo nan gaba.
5Wannan gabagadi wato begen da muke da shi baya kunyatarwa, domin kuwa an kwarara mana kaunar Allah a cikin zuciyarmu ta wurin Ruhu Mai Tsarki, da aka ba mu.
6Domin kuwa ko yayin da muke raunana, Almasihu ya mutu a lokacin da ke dai dai domin marasa ibada.
7To ai kuwa yana da wuya kwarai wani mutum ya yarda ya mutu don mutumin kirki ma. Watakila, wani na iyayin kasada ya yarda ya mutu don nagarin mutum.
8Amma Allah ya tabbatar mana da kaunarsa a gare mu, don kuwa tun muna masu zunubi, Almasihu ya mutu domin mu.
9Balle ma yanzu, da muka barata ta wurin jininsa, za mu sami tsira daga fushin Allah.
10Domin kuwa, in tun muna makiya, aka sulhunta mu da Allah ta wurin mutuwar Dansa, balle ma, yanzu da muka sami sulhu, zamu sami tsira ta wurin ransa.
11Bama haka kadai ba, amma muna murna a cikin Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu, wanda ta wurinsa ne muka sami wannan sulhu.

Read Romawa 5Romawa 5
Compare Romawa 5:3-11Romawa 5:3-11