Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Romawa - Romawa 15

Romawa 15:7-13

Help us?
Click on verse(s) to share them!
7Domin ku karbi juna, kamar yadda Yesu ma ya karbe ku domin a daukaka Allah.
8Saboda na ce an mai da Almasihu bawan kaciya a madadin gaskiyar Allah. Ya yi wannan ne don a tabbatar da alkawarai da aka ba kakanin kakaninmu.
9Domin Al'umai su daukaka Allah saboda jinkansa, kamar yadda ya ke a arubuce, “Domin ta haka zan yabe ka cikin Al'umai in yi wakar yabon sunanka.”
10Kuma an ce. “Ku yi faranciki, ku Al'ummai tare da mutanensa.”
11Kuma.” Ku yabi Ubangiji, ku dukan Al'ummai; bari dukan mutane su yabe shi.”
12Kuma, Ishaya ya ce “Za a sami tsatson Yessi, wanda zai tashi ya yi mulki a kan Al'umai, Al'umai za su sami karfin hali a cikinsa.”
13Yanzu Allah mai karfafawa ya cika ku da dukkan farin ciki salama, saboda da bangaskiyarku, domin ku sami cikkakiyar karafafawa, ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.

Read Romawa 15Romawa 15
Compare Romawa 15:7-13Romawa 15:7-13