Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Markus - Markus 9

Markus 9:33-39

Help us?
Click on verse(s) to share them!
33Sai suka zo kafarnahum. A lokacin da ya ke cikin gida, ya tambayi Al'majiransa, Menene ku ke magana a kansa a hanya?
34Amma suka yi shiru. don suna gardama da junansu akan hanya, a kan wane ne mafi girma.
35Sai ya zauna, ya kira al'majiransa goma sha biyu, yace masu duk wanda ya ke so ya zama na fari, dole ya kankantar da kansa, sa'annan ya bautawa sauran duka.
36Sai ya dauko karamin yaro a hannunsa ya sa shi a tsakiyarsu. Ya rumgome shi a kafadarsa ya ce masu.
37Dukan wanda ya karbi dan karamin yaron nan a cikin sunana ni ya karba, kuma dukan wanda ya karbi wani, ni ya karba, bai kuma karbeni ni kadai ba, duk da wanda ya aiko ni.”
38Sai Yahaya ya ce masa, Malam mun ga wani yana fitar da aljanu da sunanka mun yi kokari mu hana shi domin ba ya tare da mu.
39Sai Yesu ya ce masu ku kyale shi domin babu wanda zai yi irin wannan babban aikin, sa'annan ya fadi wasu maganganu mara sa kyau a kanmu.

Read Markus 9Markus 9
Compare Markus 9:33-39Markus 9:33-39