Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 25

Ayyukan Manzanni 25:12-27

Help us?
Click on verse(s) to share them!
12Bayan Festas ya tattauna da majalisa ya amsa ya ce, “Kana kira ga Kaisar; za ka tafi wurin Kaisar.”
13Bayan wadansu kwanaki, sarki Agaribas da Barniki suka iso Kaisariya domin su ziyarci Festas.
14Da ya kasance kwanaki da yawa, Festas ya fada wa sarki labarin Bulus ya ce, “Akwai wani mutum dan sarka da Filikus ya bari a kurkuku.
15Sa'anda nake a Urushalima, babban firist da dattawan Yahudawa suka kawo kararsa gare ni, suka roka a kashe shi.
16Game da wannan na amsa na ce masu, ba al'adar Romawa ba ce a ba da mutum tagomashi; sai wanda ake kararsa an bashi zarafi ya kare kansa a gaban masu kararsa, ya kuma bada hujjojinsa game da kararakin.
17Saboda haka, da duk suka taru ban bata lokaci ba, washegari na zauna a kujerar shari'a, na ba da umarni a kawo mutumin.
18Da masu karar suka fadi kararsu, sai na fahimci karar ba wani muhimmin abu a cikinta.
19Sai dai na ga cewa jayayya ce tsakanin su ta addini a kan wani Yesu da ya mutu, wanda Bulus ya ce yana da rai.
20Na rasa yadda zan bincike wannan al'amarin, sai na tambaye shi ko zai je Urushalima a shari'anta shi kan wadannan abubuwa.
21Amma da Bulus ya nemi a lura da shi, Kaisar ya shari'anta shi, sai na ba da umarni a ajiye shi har sai na aika shi wurin Kaisar.”
22Agaribas yace wa Festas. “Zan so ni ma in saurari mutumin nan.” “Gobe za ka ji shi,” in ji Fostus.
23Washegari Agaribas da Barniki suka zo tare da kasaitaccen taro suka shiga dakin taro tare da hafsoshi da shugabanin gari. Da Festas ya ba da umarni, aka fito da Bulus wurinsu.
24Festas ya ce, “Sarki Agaribas da dukanku da kuke tare da mu a nan, kun ga mutumin nan, dukan Yahudawa sun gana da ni a Urushalima da nan kuma. Suna mani ihu cewa, bai chanchanta a bar shi da rai ba.
25Na gane bai yi wani abin da ya chanchanci mutuwa ba; amma saboda ya daukaka kara zuwa Kaisar, na yanke shawara in aika shi.
26Amma ba ni da wani dalili na musamman da zan rubuta wasika ga Kaisar. Saboda wannan dalili na kawo shi gabanku, masamman kai ya sarki Agaribas. Domin in sami karin abin da zan rubuta game da shi.
27Gama a ganina wauta ce in aika dan sarka ba tare da na rubuta laifi a kansa ba.”

Read Ayyukan Manzanni 25Ayyukan Manzanni 25
Compare Ayyukan Manzanni 25:12-27Ayyukan Manzanni 25:12-27