Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 24

Ayyukan Manzanni 24:13-20

Help us?
Click on verse(s) to share them!
13Don haka ba su da tabbas akan abinda suke zargina a kansa yau.
14Amma na sanar da kai, bisa ga abin da suke kira darika, haka ni ma nake bautawa Allah na kakanninmu. Na yi aminci wajen kiyaye dukan abin da ke a rubuce a Attaurat da litattafan annabawa.
15Ina sa bege ga Allah, kamar yadda za a yi tashin matattu, masu adalci da miyagu;
16a kan haka kuma, nake kokarin zama mara abin zargi a gaban Allah da mutane ina yin haka cikin dukan al'amura.
17Bayan wadansu shekaru na zo in kawo wasu sadakoki da baikon yardar rai.
18Cikin kudurin yin haka, sai wasu Yahudawa daga kasar Asiya suka iske ni a cikin ka'idodin tsarkakewa a haikali, ba da taro ko ta da hargitsi ba.
19Yakamata wadannan mutanen su zo gabarka a yau, har idan suna da wani zargi a kai na.
20In kuwa ba haka ba bari mutanennan su fada in sun taba iske ni da wani aibu a duk lokacin da na gurfana a gaban majalisar Yahudawa;

Read Ayyukan Manzanni 24Ayyukan Manzanni 24
Compare Ayyukan Manzanni 24:13-20Ayyukan Manzanni 24:13-20