Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya - Yahaya 3

Yahaya 3:7-35

Help us?
Click on verse(s) to share them!
7Kada ka yi mamaki don na ce maka, 'dole a maya haifuwar ka.'
8Iska takan hura duk inda ta ga dama. Ka kan ji motsin ta, amma ba ka san inda ta fito ko inda za ta tafi ba. Haka duk wanda aka haifa daga Ruhu.”
9Nikodimu ya amsa yace masa, “Yaya wannan zai yiwu?”
10Yesu ya amsa yace masa, “Kai malami ne a Israila amma ba ka san wadannan al'amura ba?
11Hakika, hakika, ina gaya maka, muna fadin abubuwan da muka sani, kuma muna shaida abubuwan da muka gani. Duk da haka ba ku karbi shaidar mu ba.
12Idan na gaya maka abubuwan da ke na duniya amma baka gaskata ba, to yaya zaka gaskata idan na gaya maka abubuwa na sama?
13Babu wanda ya taba hawa zuwa sama sai dai shi wanda ya sauko daga sama: wato Dan Mutum.
14Kamar yadda Musa ya ta da maciji a jeji, haka ma dole a ta da Dan Mutum
15domin dukan wadanda suka bada gaskiya gareshi su sami rai na har abada.
16Gama Allah ya kaunaci duniya sosai, har ya ba da makadaicin Dansa, domin duk wanda ya bada gaskiya gareshi, kada ya mutu, amma ya samu rai madawwami.
17Gama Allah bai aiko da Dansa cikin duniya domin ya kayar da duniya ba, amma domin a ceci duniya ta wurin sa.
18Duk wanda ya bada gaskiya gare shi ba a kayar da shi ba, amma duk wanda bai bada gaskiya gare shi ba an riga an kayar da shi, domin bai bada gaskiya ga sunan wannan da shi kadai ne Dan Allah ba.
19Wannan shi ne dalilin shari'ar, domin haske ya zo duniya, amma mutane suka kaunaci duhu fiye da hasken, sabili da ayyukan su na mugunta ne.
20Domin duk wanda ke mugayen ayyuka ya ki haske, kuma baya zuwa wurin hasken domin kada ayyukansa su bayyanu.
21Sai dai duk wanda yake aikata gaskiya kan zo wurin hasken domin ayyukansa, da ake aiwatarwa ga Allah, su bayyanu.
22Bayan wannan, Yesu da almajiransa suka tafi kasar Yahudiya. A can ya dan zauna tare da su ya kuma yi Baftisma.
23Yahaya ma yana Baftisma a Ainon kusa da Salim domin akwai ruwa da yawa a can. Mutane na zuwa wurin sa yana masu Baftisma,
24domin a lokacin ba a jefa Yahaya a kurkuku ba tukuna.
25Sai gardama ta taso tsakanin almajiran Yahaya da wani Bayahude akan al'adun tsarkakewa.
26Suka je wurin Yahaya suka ce, “Rabbi, wanda yake tare da kai a dayan ketaren kogin Urdun, kuma ka shaida shi, duba, yana baftisma, kuma mutane duka suna zuwa wurin sa.”
27Yahaya ya amsa, “Mutum ba zai iya samun wani abu ba sai an ba shi daga sama.
28Ku da kanku zaku shaida na ce, 'Ba ni ne Almasihu ba' amma amaimakon haka, 'an aiko ni kafin shi.'
29Amaryar ta angon ce. Yanzu abokin angon, wanda ke tsaye yana saurarensa, yana murna sosai saboda muryan angon. Murnata ta cika domin wannan.
30Dole shi ya karu, ni kuma in ragu.
31Shi wanda ya fito daga sama ya fi kowa. Shi Wanda ya zo daga duniya, na duniya ne, kuma game da duniya yake magana. Shi wanda ya fito daga sama yana saman kowa.
32Ya shaida abubuwan da ya ji ya kuma gani, amma babu wanda ya karbi shaidarsa.
33Duk wanda ya karbi shaidarsa ya tabbatar Allah gaskiya ne.
34Domin duk wanda Allah ya aika kan yi magana da kalmomin Allah. Domin bai bada Ruhun da ma'auni ba.
35Uban ya kaunaci Dan, ya kuma ba da dukan komai a hanunsa.

Read Yahaya 3Yahaya 3
Compare Yahaya 3:7-35Yahaya 3:7-35