1Sai Bilatus yayi wa Yesu bulala.
2Sojojin kuwa suka saka rawanin kaya. Suka kuwa dora wa Yesu a kai suka sa mashi kaya irin na saurata.
3Suka zo wurin sa sukace, “Ranka ya dade, sarkin Yahudawa! sai suka nushe shi.
4Sai Bilatus ya sake fita waje yace masu, “Dubi, zan kawo maku mutumin domin ku sani ban same shi da wani laifi ba”,
5Yesu kuwa ya fito, da rawanin kaya da kaya irin na sarauta. Sai Bilatus yace “Ga mutumin nan”.
6Da manyan firistocin tare da yan majalisar suka ga Yesu, sai suka yi ta ihu suna cewa “A gicciye shi, A gicciye shi” Sai Bilatus yace masu, “ku dauke shi ku gicciye shi, ni kam ban same shi da wani laifi ba”.
7Sai Yahudawan sukace mashi, “Ai muna da shari'a, kuma bisa ga shari'ar ya cancanci mutuwa domin ya mai da kansa Dan Allah”.
8Da Bilatus ya ji wannan zance sai ya tsorata kwarai.
9Sai ya sake shiga fadar Gwamna, yace wa Yesu, “Daga ina ka fito?” amma Yesu bai amsa mashi ba.
10Sai Bilatus yace masa “Ba zaka yi mani magana ba? Baka san ina da iko in sake ka ba, kuma in gicciye ka?
11Yesu ya amsa masa, “Ai ba ka da iko a kaina sai dai in an baka daga sama, Saboda haka, wanda ya mika ni a gare ka shine mafi zunubi”.
12Da jin haka, sai Bilatus yayi kokari a sake shi, amma sai Yahudawa suka tada murya sukace, “In ka saki mutumin nan, kai ba abokin Kaisar bane, duk wanda ya maida kansa sarki, ya sabawa Kaisar”.
13Da Bilatus ya ji irin maganganunsu sai ya fito da Yesu waje ya kuma zauna akan kujeransa a inda ake kira “Dakalin shari'a,” a Yahudanci kuma, “Gabbata.”
14To a ran nan ana shirye shiryen idin ketarewa, da misalin sa'a ta shidda kenan, wato tsakar rana, Bilatus yace wa Yahudawan “Ga sarkin ku!”
15Su kuwa suka yi ihu, a tafi da shi, a tafi da shi, a gicciye shi, Bilatus yace masu “In gicciye sarkin ku? Sai manyan firistocin sukace “Ba mu da wani sarki sai Kaisar”.
16Sai Bilatus ya mika Yesu domin su gicciye shi.
17Sai suka tafi da Yesu, ya fito yana dauke da gicciyen zuwa wurin da ake kira “Wurin kwalluwa” da Yahudanci kuma “Golgota”.
18Suka gicciye Yesu a wurin, tare da wasu mutum biyu, daya a kowane gefe, Yesu kuwa na tsikiya.
19Bilatus kuwa ya rubuta wata alama a kan gicciyen, “YESU BANAZARE, SARKIN YAHUDAWA”.
20Yahudawa da yawa kuwa suka karanta wannan alama domin wurin da aka gicciye Yesu yana kusa da Birnin. Alamar kuwa an rubuta ta da Yahudanci, da Romanci, da Helenanci.
21Sai manyan firistocin yahudawa sukace wa Bilatus, kada ka rubuta sarkin Yahudawa, amma kace, 'wannan yace “Ni ne sarkin Yahudawa”'.
22Bilatus kuwa ya amsa, “Abinda na rubuta na rubuta kenan.”
23Bayan da sojojin suka gicciye Yesu, sai suka yayyaga rigarsa kashi hudu, kowane soja da nasa, kashin, sai kuma alkyabbar. Alkyabbar kuwa bata da dinki an saka tane daga sama har kasa.
24Sai sukace wa junansu, “Kada mu yaga alkyabbar, amma kuzo mu jefa kuri'a a kan ta mu gani ko wanene zai dauke ta, anyi haka ne domin a cika nassi cewa “Sun raba rigata a tsakaninsu, sun kuwa jefa kuri'a domin alkyabbata.