Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Romawa - Romawa 6

Romawa 6:1-11

Help us?
Click on verse(s) to share them!
1Me kuwa zamu ce yanzu? Sai mu ci gaba da yin zunubi domin Alheri ya yawaita?
2Ba zai taba faruwa ba. 'Yaya za'ace mu da muka mutu cikin zunubi mu ci gaba da rayuwa cikin sa?
3Ba ku san cewa duk wadanda aka yi masu baftisma cikin Almasihu Yesu an yi masu baftisma har ya zuwa mutuwarsa ne ba?
4An kuwa binne mu tare da shi, ta wurin baftisma cikin mutuwarsa. Haka kuma ya kasance ne domin kamar yadda Almasihu ya tashi daga matattu cikin daukakar Uba. Sakamakon haka muma zamu yi tafiya cikin sabuwar rayuwa.
5Domin kuwa idan muna tare dashi cikin kamannin mutuwarsa zamu kuwa zauna tare dashi har ga kamannin tashinsa.
6Mun kuma san cewa, an giciye wannan tsohon mutunmin nan namu tare dashi, domin a hallaka jikin zunubi. wanna kuwa ya kasance ne domin kada mu ci gaba da bautar zunubi.
7Duk kuma wanda ya mutu an ambace shi a matayin adali akan zunubi.
8Amma idan muka mutu tare da Almasihu, mun bada gaskiya zamu yi rayuwa tare dashi.
9Muna da sanen cewa an tada Almasihu daga matattu, don haka kuwa ba matacce yake ba. Mutuwa kuma bata da iko a kansa.
10Game da mutuwar da yayi ga zunubi yayi sau daya kuma domin dukka. Rayuwar da yake yi kuma yana yi wa Allah ne.
11Don haka ku ma sai ku dauki kanku a matsayin matattu ga zunubi amma rayayyu ga Allah cikin Almasihu Yesu.

Read Romawa 6Romawa 6
Compare Romawa 6:1-11Romawa 6:1-11