1Siman Bitrus, bawa da manzon Almasihu Yesu, zuwa ga wadanda suka karbi bangaskiya mai daraja kamar yadda muka karba, bangaskiya cikin adalcin Allahnmu da Yesu Almasihu.
2Bari alheri ya kasance tare da ku; bari salama ta karu ta wurin sanin Allah da na Yesu Ubangijinmu.
3Dukkan abubuwan ikon Allah na rayuwa da Allahntaka an bamu su ta wurin sanin Allah, wanda ya kira mu ta wurin daukakarsa da nagarta.
4Ta wurin wanan, ya bamu babban alkawari mai daraja. Yayi wanan ne saboda ku zama masu rabo cikin Allahntaka, yayin da ku ka kubuta daga lalacewa da ke cikin duniya saboda mugayen sha'awace sha, awace.
5Saboda wanan dalilin kuyi iyakacin kokarinku ku kara nagarta ta wurin bangaskiyarku, kuma ta wurin adalci, sani.
6Ta wurin sani ku kara da kamun kai, kuma ta wurin kamun kanku, ku kara da jimrewa, ta wurin jimrewarku, ku kara da bin Allah.
7Ta wurin bin Allah, ku kara da kauna irin ta 'yan'uwa, ta wurin kauna irin ta 'yan'uwa, ku kara kauna.
8Idan wadannan abubuwan suna cikinku, kuma suka yi girma a cikinku, baza a sami bakarare ko rashin 'ya'ya cikin sanin Ubangijinmu Yesu Almasihu ba.
9Amma duk wanda ya rasa wadannan abubuwan yana kallon abin da ke kusa ne kawai; ya makance. Ya manta da cewa an wake shi daga tsofaffin zunubansa.
10Saboda haka, 'yan'uwa, kuyi iyakacin kokari ku tabbatar da kiranku da zabenku. Idan kun yi wadannan abubuwan, baza ku yi tuntube ba.
11Ta haka zaku sami shiga cikin mulki na har'abada na Ubangijinmu da Maicetonmu Yesu Almasihu.
12Saboda haka a shirye nake kulayomi in tunashe ku game da wadannan abubuwan, ko da yake kun san su, kuma kun yi karfi cikin gaskiya yanzu.
13Ina tunani daidai ne in zuga ku da tuni game da wadannan abubuwan, tun ina cikin wannan jiki.
14Domin na sani jim kadan zan bar wannan jiki, kamar yadda Yesu Almasihu ya nuna mani.