Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - 2 Bitrus

2 Bitrus 1

Help us?
Click on verse(s) to share them!
1Siman Bitrus, bawa da manzon Almasihu Yesu, zuwa ga wadanda suka karbi bangaskiya mai daraja kamar yadda muka karba, bangaskiya cikin adalcin Allahnmu da Yesu Almasihu.
2Bari alheri ya kasance tare da ku; bari salama ta karu ta wurin sanin Allah da na Yesu Ubangijinmu.
3Dukkan abubuwan ikon Allah na rayuwa da Allahntaka an bamu su ta wurin sanin Allah, wanda ya kira mu ta wurin daukakarsa da nagarta.
4Ta wurin wanan, ya bamu babban alkawari mai daraja. Yayi wanan ne saboda ku zama masu rabo cikin Allahntaka, yayin da ku ka kubuta daga lalacewa da ke cikin duniya saboda mugayen sha'awace sha, awace.
5Saboda wanan dalilin kuyi iyakacin kokarinku ku kara nagarta ta wurin bangaskiyarku, kuma ta wurin adalci, sani.
6Ta wurin sani ku kara da kamun kai, kuma ta wurin kamun kanku, ku kara da jimrewa, ta wurin jimrewarku, ku kara da bin Allah.
7Ta wurin bin Allah, ku kara da kauna irin ta 'yan'uwa, ta wurin kauna irin ta 'yan'uwa, ku kara kauna.
8Idan wadannan abubuwan suna cikinku, kuma suka yi girma a cikinku, baza a sami bakarare ko rashin 'ya'ya cikin sanin Ubangijinmu Yesu Almasihu ba.
9Amma duk wanda ya rasa wadannan abubuwan yana kallon abin da ke kusa ne kawai; ya makance. Ya manta da cewa an wake shi daga tsofaffin zunubansa.
10Saboda haka, 'yan'uwa, kuyi iyakacin kokari ku tabbatar da kiranku da zabenku. Idan kun yi wadannan abubuwan, baza ku yi tuntube ba.
11Ta haka zaku sami shiga cikin mulki na har'abada na Ubangijinmu da Maicetonmu Yesu Almasihu.
12Saboda haka a shirye nake kulayomi in tunashe ku game da wadannan abubuwan, ko da yake kun san su, kuma kun yi karfi cikin gaskiya yanzu.
13Ina tunani daidai ne in zuga ku da tuni game da wadannan abubuwan, tun ina cikin wannan jiki.
14Domin na sani jim kadan zan bar wannan jiki, kamar yadda Yesu Almasihu ya nuna mani.
15Zan yi iyakancin kokarina kulayomi domin ku rika tunawa da abubuwan, bayan kaurata.
16Domin bamu bi labaru da aka kago na nuna wayo cikinsu ba, da muka fada maku game da iko da bayyanuwar Ubangijinmu Yesu Almasihu, amma mu shaidu ne na ikonsa.
17Gama ya karbi daukaka da daraja daga wurin Allah Uba lokacin da murya ta zo daga ikon mai daukaka cewa, “Wannan shine dana, kaunataccena, wanda nake jin dadinsa kwarai.”
18Mun ji muryar nan da ta zo daga sama, lokacin da mu ke tare da shi a dutse mai tsarki.

19Muna da wannan kalmar annabci wanda akwai tabbaci sosai, kun yi daidai idan kun mayar da hankali a kansu. Yana nan kamar fitillar da take walkiya a wuri mai duhu kafin asubahi ya zo, kuma tauraron asubahi ya tashi cikin zukatanku.
20Ku san da wannan tun da farko, cewa babu annabci da ke bisa ga fasarar mutum.
21Domin babu annabcin da ya taba zuwa ta wurin nufin mutum. Maimakon haka, Ruhu Mai Tsarki ne ke iza su, su fadi maganar Allah.