Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya - Yahaya 4

Yahaya 4:1-12

Help us?
Click on verse(s) to share them!
1Da Yesu ya sani cewa Farisawa sun ji cewa yana samun almajirai yana kuma yi masu baftisma fiye da Yahaya
2(ko da shike ba Yesu da kansa ke yin baftismar ba, amma almajiransa ne),
3ya bar Yahudiya ya koma Galili.
4Amma ya zamar masa dole ya ratsa ta Samariya.
5Ya zo wani birnin Samariya, mai suna Sika, kusa da filin da Yakubu ya ba dansa Yusufu.
6Rijiyar Yakubu na wurin. Da Yesu ya gaji da tafiyarsa sai ya zauna gefen rijiyar. Kusan karfe goma sha biyu na rana ne.
7Wata mace, Ba-Samariya ta zo domin ta dibi ruwa, sai Yesu ya ce mata, “Ba ni ruwa in sha.”
8Gama almajiransa sun tafi cikin gari don sayen abinci.
9Sai ba-Samariyar tace masa, “Yaya kai da kake Bayahude kake tambaya ta ruwan sha, ni da nike 'yar Samariya?” Domin Yahudawa ba su harka da Samariyawa.
10Sai Yesu ya amsa yace mata, “In da kin san kyautar Allah, da shi wanda yake ce da ke, 'Ba ni ruwan sha,' da kin roke shi, sai kuma ya ba ki ruwan rai.”
11Matar tace masa, “Mallam, ga shi ba ka da guga, kuma rijiyar tana da zurfi. Ina za ka samu ruwan rai?
12Ai ba ka fi Ubanmu Yakubu ba, ko ka fi shi, shi wanda ya ba mu rijiyar, shi kansa kuma ya sha daga cikin ta, haka kuma 'ya'yansa da shanunsa?”

Read Yahaya 4Yahaya 4
Compare Yahaya 4:1-12Yahaya 4:1-12