19Idan har sun bada ku, kada ku damu da yadda za ku yi magana, ko kuwa abin da za ku fada, domin za a ba ku abin da za ku fada a lokacin.
20Domin ba ku ne kuke magana ba, Ruhun Ubanku ne yake magana ta bakinku.
21Dan'uwa zai ba da dan'uwansa a kashe shi, uba kuwa dansa. 'Ya'ya kuma za su tayarwa iyayensu, har su sa a kashe su.
22Kowa kuma zai ki ku saboda sunana. Amma duk wanda ya jure har karshe, zai tsira.
23In sun tsananta maku a wannan gari, ku gudu zuwa na gaba. Hakika ina gaya maku, kafin ku gama zazzaga dukan garuruwan Isra'ila, Dan Mutum zai zo.
24Almajiri ba ya fin malaminsa, bawa kuma ba yafin ubangijinsa.
25Dai dai ne almajiri ya zama kamar malaminsa, bawa kuma kamar ubangijinsa. In har sun kira mai gida Ba'alzabuba, za su kuma bata mutanen gidansa!
26Don haka kada kuji tsoron su, domin ba abin da yake boye da ba za a bayyana ba.
27Abin da nake fada maku a asirce, ku fada a sarari. Abin da kuma kuka ji a cikin rada, ku yi shelarsa daga kan soraye.
28Kada ku ji tsoron masu kisan jikin mutum, amma ba sa iya kashe rai. Sai dai ku ji tsoron wannan da yake da ikon kashe jiki ya kuma jefa rai cikin jahannama.
29Ba 'yan tsuntsaye biyu ake sayarwa akan kobo ba? Ba ko daya a cikin su da zai fadi kasa ba tare da yardar Ubanku ba.
30Ai, ko da gashin kan ku ma duk a kidaye yake.
31Kada ku ji tsoro. Gama darajarku ta fi ta tsuntsaye masu yawa.