1A kwanakin nan Yahaya Mai baftisma ya zo, yana wa'azi a jejin Yahudiya yana cewa,
2“Ku tuba, domin mulkin sama ya kusa.”
3Wannan shine wanda annabi Ishaya ya yi maganarsa, ya ce, “Muryar wani mai kira a jeji yana cewa, 'Ku shirya wa Ubangiji hanyarsa, ku daidaita tafarkunsa.”
4Yahaya kuwa yana sanye da tufa ta gashin rakumi, yana kuma daure da damarar fata, abincinsa kuwa fara ne da zuman jeji.
5Sai mutanen Urushalima, da na dukan Yahudiya, da na duk kasashen bakin Kogin Urdun, suka yi ta zuwa wurin sa.
6Ya yi masu baftisma a Kogin Urdun, yayinda suke furta zunubansu.
7Amma da ya ga Farisawa da Sadukiyawa da yawa, suna fitowa domin a yi masu baftisma, sai ya ce masu, “Ku 'ya'yan macizai masu dafi, wa ya gargade ku ku guje wa fushi mai zuwa?
8Ku ba da 'ya'ya da za su nuna tubanku.
9Kada kuwa ku dauka a ranku cewa, 'Ibrahim ne ubanmu.' Domin ina gaya maku, Allah yana da iko ya ta da wa Ibrahim 'ya'ya daga cikin duwatsun nan.
10Ko yanzu ma an sa gatari a gindin bishiyoyin. Saboda haka duk bishiyar da ba ta ba da 'ya'ya masu kyau ba, sai a sare ta a jefa a wuta.
11Na yi maku baftisma da ruwa, zuwa tuba. Amma mai zuwa baya na, ya fi ni girma, wanda ko takalmansa ma ban isa in dauka ba. Shi ne zai yi maku baftisma da Ruhu Mai Tsarki, da kuma wuta.
12Kwaryar shikarsa na hannunsa, zai kuwa share masussukarsa sarai, ya tara alkamarsa ya sa a rumbunsa, amma zai kona buntun da wutar da ba za a iya kashewa ba.”
13Sai Yesu ya zo daga kasar Galili, ya je Kogin Urdun wurin Yahaya, domin ya yi masa baftisma.
14Amma Yahaya ya yi ta kokarin ya hana shi, yana cewa, “Ni da nake bukatar ka yi mani baftisma, ka zo gare ni?”
15Yesu ya amsa masa ya ce, “Bari ya zama haka a yanzu, domin a cika dukan adalci.” Sai Yahaya ya yarje masa.
16Bayan da aka yi masa baftisma, Yesu ya fito nan da nan daga cikin ruwan, sai kuma sammai suka bude masa. Ya ga Ruhun Allah yana saukowa kamar kurciya, ya sauko a kansa.
17Duba, wata murya daga sammai tana cewa, “Wannan shi ne kaunataccen Da na. Wanda ya gamshe ni sosai.”