50Amma Yesu ya ce, “Kada ku hana shi yin haka, domin dukan wanda ba ya gaba da ku, yana tare da ku.”
51Sa'adda rana ta kusato da zai hawo zuwa sama, ya kudurta sosai zai tafi Urushalima.
52Ya aiki wadansu manzanni su shirya wuri dominsa kafin ya zo. Suka shiga wani kauye a cikin kauyen Samariya domin su shirya masa wuri a can.
53Amma mutanen can ba su karbe shi ba tun da ya ke Urushalima zai tafi.
54Sa'adda biyu daga cikin almajiransa, wato Yakubu da Yahaya suka ga haka, suka ce, “Ubangiji, kana so mu umarci wuta ta sauko daga sama, ta hallaka su?”
55Amma, ya juya ya tsauta masu.
56Sai suka tafi wani kauye dabam.
57Da suna cikin tafiya a kan hanya, sai wani mutum ya ce da shi, “Zan bi ka dukan inda za ka tafi.”
58Yesu ya amsa masa, “Dila suna da ramuka a kasa inda za su shiga, tsuntsaye kuma suna da sheka, amma Dan Mutum ba shi da inda zai kwanta.”
59Yesu, ya ce da wani mutumin kuma, “Ka biyo ni.” Amma mutumin ya ce, “Ubangiji, ka bari in koma gida in bizine mahaifina tukuna.”
60Amma Yesu ya ce masa, “Ka bar matattu su bizine matattunsu; amma kai ka tafi ka yi wa mutane shelar mulkin Allah a ko'ina.”