Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 7

Luka 7:11-43

Help us?
Click on verse(s) to share them!
11Wani lokaci bayan wannan, ya zama Yesu yana tafiya wani gari da ake kira Na'im. Almajiransa su na tare da shi, da kuma taron mutane masu yawa.
12Sa'adda ya kusa da kofar garin, sai ga wani matacce ana dauke da shi. Kuma shi kadai ne da a wurin mahaifiyarsa. Ita kuwa gwauruwa ce, mutane da dama daga cikin gari suna tare da ita.
13Da ganin ta, sai Ubangiji ya cika da tausayi a game da ita ya ce da ita, “Kada ki yi kuka.”
14Sai ya zo ya taba makarar, sai masu dauke da shi su ka tsaya. Ya ce 'Saurayi na ce ma ka ka tashi.”
15Sai mataccen ya tashi ya fara yin magana. Sai Yesu ya ba mahaifiyar danta.
16Sai tsoro ya kama su duka. Su ka kama yabon Allah, su na cewa, “An ta da wani annabi mai girma a cikinmu” kuma “Allah ya dubi mutanensa.”
17Wannan labari na Yesu, ya ba zu a cikin dukan Yahudiya da yankuna da su ke kewaye.
18Almajiran Yahaya suka gaya masa dukan wadannan abubuwa.
19Sai Yahaya ya kira biyu daga cikin almajiransa, ya aike su wurin Ubangiji, suka ce da shi, “Kai ne mai zuwan nan, ko akwai wani wanda za mu saurari zuwansa?”
20Sa'adda suka zo kusa da Yesu, sai mutanen suka ce, “Yahaya Mai Baftisma, ya aiko mu, mu tambaya, “Kai ne mai zuwan nan, ko akwai wani wanda za mu saurari zuwansa?”
21A cikin wannan lokaci, ya warkar da mutane da yawa daga cututtuka da matsaloli da miyagun ruhohi. Makafi da yawa sun sami ganin gari.
22Yesu, ya amsa ya ce masu, “Bayan kun tafi, ku ba Yohanna rahoton abin da ku ka ji da abin da ku ka gani. Makafi suna ganin gari, guragu suna tafiya, ana kuma tsarkake kutare. Kurame suna ji, ana tayar da matattu, ana gaya wa matalauta labari mai dadi.
23Mai albarka ne mutumin da ya tsaya a kan ba da gaskiya gare ni saboda ayukan da na ke yi.”
24Bayan da mutanen da Yahaya ya aiko suka tafi, Yesu ya fara yi wa taron magana game da Yahaya. “Me ku ka tafi ku gani a cikin hamada, ciyawa wadda iska ta ke girgizawa?
25Amma me ku ka tafi domin ku gani, mutum mai saye da tufafi masu taushi? Duba mutanen da su ke saye da tufafi masu daraja, kuma suna rayuwa cikin jin dadi suna fadar sarakuna.
26Amma me ku ka tafi domin ku gani, annabi ne? I, ina gaya ma ku, ya ma fi annabi.
27Wannan shine wanda aka rubuta a kansa, “Duba, ina aika manzo na a gabanka, wanda za ya shirya maka hanya a gabanka.
28Ina gaya maku, a cikin wadanda mata suka haifa, ba wanda ya fi Yahaya girma. Duk da haka, wanda ya fi kankanta a mulkin Allah, ya fi shi girma.
29Sa'anda dukan mutane suka ji haka, har da ma su karbar haraji, suka shaida Allah mai adalci ne. Su na cikin wadanda Yahaya ya yi wa baftisma.
30Amma Farisawa da wadanda su ke kwararru a cikin shari'ar Yahudawa, wadanda ba shi ne ya yi masu baftisma ba, suka yi watsi da hikimar Allah don kansu.
31Sa'annan Yesu ya ce, “Da me zan kamanta mutanen wannan zamani? Da me suka yi kama?
32Suna kama da yaran da suke wasa a kasuwa, wadanda suke magana da junansu suna cewa, “Mun yi maku busa, ba ku yi rawa ba. Mun yi makoki, ba ku yi kuka ba.”
33Haka, Yahaya ya zo, bai ci gurasa ba, bai sha ruwan inabi ba, amma ku ka ce, 'Aljani ne yake mulkinsa.
34Dan Mutum, ya zo, yana ci, yana sha, amma, kuka ki shi, kuna cewa dubi mutum mai hadama, mai shan ruwan inabi da yawa, abokin masu karbar haraji da masu zunubi!
35Amma hikimar Allah tana shaidar dukan 'yayanta.”
36Wata rana wani Bafarise, ya roki Yesu ya je ya ci abinci tare da shi. Bayan da Yesu ya shiga gidan Bafarisen, ya zauna a teburi domin ya ci abinci.
37Sai ga wata mace mai zunubi, ta fito daga cikin birni. Sa'anda ta ji labari Yesu yana gidan Bafarisen, domin ya ci abinci. Ta dauki tandun mai na alabastar mai kamshi.
38Ta tsaya kusa da Yesu tana kuka. Ta fara jika kafafunsa da hawayenta, tana shafe kafafunsa da gashin kanta. Tana yi wa kafafunsa sumba, tana shafe su da turare.
39Sa'anda Bafarisen da ya gaiyaci Yesu, ya ga haka, sai ya yi tunani a cikin ransa, da cewa, “In da wannan mutum annabi ne, da ya gane ko wacce irin mace ce, wannan da take taba shi, ita mai zunubi ce.”
40Yesu ya amsa ya ce masa, “Siman, ina so in gaya maka wani abu.” Ya ce, “malam sai ka fadi!”
41Yesu ya ce, “wani mutum mai ba da bashi yana bin wadansu mutane su biyu kudi, yana bin dayan sule dari, dayan kuma yana bin sa sule hamsin.
42Da yake ba su da kudin da za su iya biyan sa, sai ya yafe masu, su duka biyu. A cikin su biyu, wanne ne zai fi nuna kauna ga wannan mutum?”
43Siman ya amsa ya ce, “Ina tsammani wanda ya yafe wa kudi da yawa.” Yesu ya amsa ya ce masa, “Ka shari'anta dai dai.”

Read Luka 7Luka 7
Compare Luka 7:11-43Luka 7:11-43