Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 2

Luka 2:1-5

Help us?
Click on verse(s) to share them!
1Ananan cikin kwanakin, sai Kaisar Augustas ya yi shela ya umarta a kidaya dukan mutane da ke zaune a cikin duniya.
2Wannan itace kidaya ta farko da aka yi lokacin da Kiriniyus yake mulkin Suriya.
3Sabili da haka, kowa ya koma garinsa domin a yi masa rijista domin kidayan.
4Yusufu kuma ya tashi ya bar birnin Nazarat zuwa garin Baitalami da ke Yahudiya, wanda ake kuma kira birnin Dauda, domin shi daga zuriyar iyalin Dauda ne.
5Ya je can ya yi rijista tare da Maryamu, wadda yake tashi tana kuma da juna biyu.

Read Luka 2Luka 2
Compare Luka 2:1-5Luka 2:1-5