Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 1

Luka 1:5-36

Help us?
Click on verse(s) to share them!
5A cikin zamanin Hirudus, Sarkin Yahudiya, akwai wani firist mai suna Zakariya, daga yankin Abija. Matarsa daga cikin yaya mata na zuriyar Haruna ce, kuma sunan ta Alisabatu ne.
6Dukan su biyu masu adalci ne a gaban Allah; marasa zargi a tafiyarsu cikin dukan dokoki da farilan Ubangiji.
7Amma ba su da da, domin Alisabatu ba ta haihuwa, kuma a wannan lokacin dukansu sun tsufa kwarai.
8Ya zama kuma a lokacin da Zakariya yana gaban Allah, yana yin hidimar sa ta firist bisa ga tsari da ka'idar aikinsa.
9Bisa ga al'adar zaben firist da zai yi hidima, an zabe shi ta wurin kuri'a ya shiga cikin haikalin Ubangiji domin ya kona turare.
10Dukan taron Jama'a suna addu'a a waje a sa'adda ake kona turaren.
11A lokacin, mala'ikan Ubangiji ya bayana a gare shi yana tsaye a gefen daman bagadi na turaren.
12Zakariya ya firgita sa'adda ya gan shi; tsoro ya kama shi.
13Amma mala'ikan ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, Zakariya, domin an ji addu'ar ka. Matar ka Alisabatu za ta haifa maka da. Za ka kira sunansa Yahaya.
14Za ka yi murna da farin ciki, kuma da yawa za su yi murna da haifuwarsa.
15Domin zai zama mai girma a gaban Ubangiji. Ba zai sha ruwan inabi ba ko wani abu mai sa maye, kuma zai cika da Ruhu Mai Tsarki tun daga cikin cikin mahaifiyarsa.
16Kuma mutanen Isra'ila da yawa za su juya zuwa ga Ubangiji Allahnsu.
17Zai yi tafiya a gaban Unbangiji a cikin ruhu da ikon Iliya. Zai yi haka domin ya juya zuciyar Ubanni zuwa ga 'ya'yansu, domin marasa biyayya su yi tafiya a cikin tafarkin adalai. Don ya shirya wa Ubangiji mutanen da aka shirya dominsa.”
18Zakariya ya ce wa mala'ikan, “Ta yaya zan san wannan? Ga shi na tsufa kuma matata tana da shekaru da yawa.”
19Mala'ikan ya amsa ya ce masa, “Nine Jibra'ilu, wanda ke tsaye a gaban Allah. An aiko ni in gaya maka wannan labari mai dadi.
20Kuma duba, za ka zama bebe, ba za ka iya magana ba, sai ran da wadannan abubuwa suka cika. Ya zama haka domin ba ka gaskanta da kalmomina ba, wadanda za su cika a daidai lokacin.”
21Sa'adda mutane suke jiran Zakariya. Sun yi mamaki yadda ya dauki lokaci sosai a cikin haikali.
22Amma da ya fita, bai iya yin magana da su ba. Sun gane da cewa ya ga wahayi lokacin da yake cikin haikali. Ya ci gaba da yi masu alamu, ba ya magana.
23Ya zama bayan da kwanakin hidimarsa suka kare, ya tafi gidansa.
24Bayan kwanakin nan, matarsa Alisabatu ta samu juna biyu. Ta boye kanta har na watani biyar. Ta ce,
25“Wannan shi ne abin da Allah ya yi mani da ya dube ni domin ya dauke kunyata a gaban jama'a.”
26A cikin watan ta na shidda, an aiki Mala'ika Jibra'ilu daga wurin Allah zuwa wani birni a Galili mai suna Nazarat,
27zuwa ga wata budurwa wanda aka ba da ita ga wani mutum mai suna Yusufu. Shi dan zuriyar Dauda ne, kuma ana kiran budurwar Maryamu.
28Ya zo wurin ta ya ce, “A gaishe ki, ke da ki ke da tagomashi sosai! Ubangiji yana tare da ke.
29Amma ta damu kwarai da wadannan kalmomi sai ta yi tunani ko wacce irin gaisuwa ce wannan.
30Mala'ikan ya ce mata, “Kada ki ji tsoro, Maryamu, domin kin samu tagomashi a wurin Allah.
31Duba, za ki sami juna biyu, za ki haifi da. Za ki kira sunansa 'Yesu'.
32Zai zama mai girma, kuma za a ce da shi Dan Allah Madaukaki. Ubangiji Allah zai ba shi kursiyin ubansa Dauda.
33Zai yi mulkin dukkan gidan Yakubu har abada, kuma mulkinsa ba shi da iyaka.”
34Maryamu ta ce wa mala'ikan, “Yaya wannan zai faru, tun da shike ni ban san namiji ba?”
35Mala'ikan ya amsa ya ce mata, “Ruhu Mai-tsarki zai sauko a kan ki, kuma ikon Madaukaki zai lullube ki. Sabili da haka, za a kira mai tsarkin da za ki haifa Dan Allah.
36Ki kuma duba, ga 'yar'uwarki Alisabatu ta samu juna biyu a tsufanta. Watannin ta shida kenan, ita wadda aka kira ta bakarariya.

Read Luka 1Luka 1
Compare Luka 1:5-36Luka 1:5-36