Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 16

Luka 16:8-18

Help us?
Click on verse(s) to share them!
8Sai maigida ya yaba wa wakilin nan marar gaskiya saboda wayonsa. Gama 'ya'yan zamanin nan a ma'ammalar su da mutanen zamaninsu sun fi 'ya'yan haske wayo.
9Ina gaya maku ku yi abuta ta dukiya ta rashin gaskiya, saboda idan ya kare, su karbe ku a gidaje masu dauwama.
10Wanda yake da aminci a karamin abu, mai aminci ne a babban abu, wanda yake marar gaskiya a karamin abu, marar gaskiya ne a babban abu.
11Idan fa ba ku yi aminci da dukiya mara adalci ba, wa zai amince maku da dukiya ta gaskiya?
12Idan kuma ba ku yi aminci da kudin wani ba, wa zai ba ku kudin da ke naku?
13Ba bawan da zai iya bauta wa iyayengiji biyu, ko dai ya ki daya, ya so daya ko kuwa ya amince wa dayan, ya raina dayan. Ba za ku iya bauta wa Allah ku kuma bauta wa dukiya ba.”
14Da Farisawa da ke da kaunar kudi suka ji dukan wadannan abubuwa, suka yi masa ba'a.
15Sai ya ce masu, “Ku ne masu baratar da kanku a gaban mutane, amma Allah ya san zuciyarku. Abin da mutane suke girmamawa kwarai abin kyama ne a gun Allah.
16Attaura da litattafan annabawa suna nan har zuwan Yahaya. Tun daga lokacin nan ake yin bisharar mulkin Allah, kowa kuma yana kokarin kutsawa zuwa cikinta.
17Duk da haka, zai fi sauki sama da kasa su shude, da ko digo daya na attaura ya shude.
18Duk wanda ya saki matansa ya auri wata ya aikata zina, kuma wanda ma ya auri sakakkiya ya aikata zina.

Read Luka 16Luka 16
Compare Luka 16:8-18Luka 16:8-18