Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 10

Ayyukan Manzanni 10:13-24

Help us?
Click on verse(s) to share them!
13Sai murya ta yi magana da shi; “Tashi, Bitrus, yanka ka ci”
14Amma Bitrus ya ce “Ba haka ba, Ubangiji, gama ban taba cin abu mara tsarki ko mai kazanta ba.”
15Amma muryar ta sake zuwa masa karo na biyu kuma; “Abinda Allah ya tsarkake, kada ka kira shi kazantacce.”
16Wannan ya faru sau uku; nan da nan sai aka dauki tasar zuwa sama.
17A yayin da Bitrus na cikin rudani game da ma'anar wahayin da ya gani, sai ga mutanen da Karniliyas ya aika suna tsaye a bakin kofar gidan, bayan sun tambayi hanyar zuwa gidan,
18Kuma suka yi sallama suna tambaya ko Saminu wanda ake kira Bitrus ya sauka a nan.
19A yayin da Bitrus yana kan tunani akan wahayin, Ruhu ya ce masa, “Duba, mutane uku na neman ka.”
20Tashi ka sauka ka tafi tare da su. Kada ka yi jinkirin tafiya tare da su, domin Nine na aike su.”
21Bitrus kuwa ya sauko wurin mutanen ya ce, “Ni ne wanda kuke nema. Me ya sa kuka zo?”
22Suka ce, “Shugaban soja mai suna Karniliyas, adalin mutum kuma mai bautar Allah, yana da kyakkyawar shaida a dukan al'umman Yahudawa, shi ne wanda mala'ika mai tsarki na Allah ya aika domin ka zo gidansa, ya ji sako daga wurinka.”
23Sai Bitrus ya gayyace su su zo ciki kuma su zauna tare da shi. Washegari sai ya tafi tare da su, kuma wadansu 'yan'uwa daga Yafa suka raka shi.
24Kashegari suka shiga Kaisariya, Karniliyas kuwa yana jiran su; har ma ya gayyaci 'yan'uwansa da kuma abokansa na kusa.

Read Ayyukan Manzanni 10Ayyukan Manzanni 10
Compare Ayyukan Manzanni 10:13-24Ayyukan Manzanni 10:13-24