Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya - Yahaya 4

Yahaya 4:47-54

Help us?
Click on verse(s) to share them!
47Da ya ji cewa Yesu ya bar Yahudiya ya koma Galili, sai ya tafi wurin Yesu ya roke shi ya sauko ya warka da dansa wanda ke bakin mutuwa.
48Yesu yace masa, “Idan ba ku ga alamu da mu'ujizai ba, ba za ku gaskata ba.”
49Ma'aikacin ya ce masa, “Mallam, ka sauko kafin da na ya mutu.”
50Yesu yace masa, “Je ka. Dan ka ya rayu.” Mutumin ya gaskata maganar da Yesu ya gaya masa, Sai yayi tafiyarsa.
51Yayin da yake sauka kasa, bayinsa suka same shi, suna cewa, danka yana raye.
52Sai ya tambaye su sa'ar da ya fara samun sauki. Suka amsa masa, “Jiya a sa'a ta bakwai zazabin ya bar shi.”
53Sai Uban ya gane cewa wannan sa'a ce Yesu ya ce masa, “Jeka, danka na raye.” Sabili da haka, shi da dukan gidansa suka bada gaskiya.
54Wannan ce alama ta biyu da Yesu ya yi bayan da ya bar Yahudiya zuwa Galili.

Read Yahaya 4Yahaya 4
Compare Yahaya 4:47-54Yahaya 4:47-54