Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Romawa - Romawa 2

Romawa 2:7-15

Help us?
Click on verse(s) to share them!
7Ga wadanda kuma suka nace da yin ayyukan alheri ba fasawa, sun samarwa kansu, yabo da daraja, da rai na har'abada.
8Amma ga masu son kai, wadanda suka ki yin biyayya ga gaskiya, suka yiwa rashin adalci biyayya, fushi da hasala mai zafi zai afko masu.
9Allah kuma zai sauko da bala'i da bakin ciki ga dukkan rayukan da suka aikata mugunta, ga Yahudawa da fari, sannan kuma Hellinawa.
10Amma yabo daraja da salama zasu kasance ga dukkan wadanda suka aikata ayukan alheri, ga Yahudawa da fari sannan Hellanawa.
11Domin kuwa Allah ba mai tara bane.
12Ga wadanda suka yi zunubi batare da shari'aba, zasu hallaka ba tare da shari'a ba, ga wadanda suka yi zunubi cikin shari'a kuma za'a hukunta su bisa ga shari'a.
13Domin kuwa ba masu jin shari'ar ne masu adalci agaban Allah ba, amma masu aikatawa ne zasu samu barata.
14Gama al'umai da basu san shari'a ba, bisa ga dabi'a sun yi abinda ke na shari'a, sun kuma zame wa kansu shari'a, koda shike basu da shari'ar.
15Dalilin haka kuwa sun nuna cewa ayukan da shari'a take bukata na nan a rubuce a zuciyarsu. lamirinsu kuma na yi masu shaida, tunanainsu kuma, ko dai yana kashe su, ko kuma yana karesu.

Read Romawa 2Romawa 2
Compare Romawa 2:7-15Romawa 2:7-15