Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 21

Luka 21:17-36

Help us?
Click on verse(s) to share them!
17Kowa zai ki ku saboda sunana.
18Amma ba ko gashin kanku da zai hallaka.
19A cikin hankurin ku za ku ribato rayukanku.
20Sa'adda ku ka ga Urushalima tana kewaye da sojoji, sai ku sani da cewa faduwarta ta yi kusa.
21Sai wadanda su ke Yahudiya su gudu zuwa kan tuddai, wadanda suke tsakiyar gari kuma su tafi, kada su bar wadanda suke kauyuka su shigo ciki.
22Gama wadannan ranakun ramako ne, saboda duka abubuwan da aka rubuta su cika.
23Kaiton wadanda suke da juna biyu da masu ba da mama a wannan kwanakin! Gama za a sha kunci mai girma a kasan, da fushi kuma zuwa ga mutanen nan.
24Za su fadi ta kaifin takobi kuma za a kai su cikin bauta ga dukan kasashe, al'ummai za su tattake Urushalima, har ya zuwa lokacin al'ummai ya cika.
25Za a ga alamomi cikin rana da wata da kuma taurari. A duniya kuma, al'ummai za su sha kunci, za su rude saboda rurin teku da rakuman ruwa.
26Mutane za su suma da tsoro da kuma da tunanin abubuwa da za su abko wa duniya. Gama za a girgiza ikokin sammai.
27Sa'annan za su ga Dan Mutum yana zuwa a cikin gajimarai da iko da daukaka mai girma.
28Amma sa'adda wadannan abubuwa suka fara faruwa, tashi saye, sai ku daga kanku sama, saboda ceton ku ya kusato.”
29Yesu ya bada misali, “Duba itacen baure, da duka itatuwa.
30Sa'adda su ke fitar da ganye, za ku gani da kanku cewa bazara ta yi kusa kuma.
31Haka kuma, sa'adda ku ka ga wadannan abubuwa suna faruwa, ku sani cewa mulkin Allah ya yi kusa.
32Gaskiya, na ke gaya maku, wannan zamani ba za ya shude ba, sai duka abubuwan nan sun faru.
33Sama da kasa za su shude, amma maganata ba za ta shude ba.
34Amma ku lura da kanku, domin kada ku nawaita zuciyarku da tararradin duniya da shayeshaye da damuwa ta rayuwa. Gama ranar za ta zo babu shiri
35kamar tarko. Gama zai zo akan kowa da ke rayuwa a fuskar dukan duniya.
36Amma ku zama a fadake kowanne lokaci, kuna addu'a domin ku iya samun karfin tserewa dukan wadannan abubuwa da za su faru, da kuma yadda za ku tsaya a gaban Dan Mutum.”

Read Luka 21Luka 21
Compare Luka 21:17-36Luka 21:17-36