39Kuma ku san wannan, da mai gida ya san lokacin da barawo zai zo, ba zai bari a fasa masa gida a shiga ba.
40Sai ku zauna da shiri fa domin ba ku san lokacin da Dan Mutum zai dawo ba.”
41Sai Bitrus ya ce masa, “Ubangiji, mu ka ke fadawa wannan misali, ko ga kowa da kowa ne?”
42Sai Ubangiji ya ce, “Wanne shugaba ne, mai aminci, mai hikima kuma wanda ubangijinsa za ya damka bayinsa a hannunsa, domin ya kula da su, ya ba su abincinsu a kan lokaci?
43Mai albarka ne wannan bawa, wanda ubangijinsa za ya tarar da shi yana yin abin da aka sa shi ya yi.
44Hakika, ina gaya maku, zai danka dukan malakarsa a gareshi.
45Amma idan wannan bawa, ya ce a cikin zuciyarsa, 'Ubangiji na yayi jinkirin dawowa,' sai ya fara dukan bayin, maza da mata abokan bautarsa, ya ci ya sha, ya bugu,
46ubangijin bawan nan zai dawo a lokacin da bawan bai sa tsammani ba, kuma a cikin lokacin da bai sani ba, ya daddatsa shi gunduwa-gunduwa, ya kuma hada shi da marasa aminci.
47Bawan nan, ya san halin ubagijinsa, amma bai shirya yayi abin da ubangijinsa yake so ba. Zai sha duka da bulala da yawa.
48Amma shi wanda bai sani ba, kuma yayi abin da ba daidai ba, ba zai sha duka da bulala da yawa ba. Dukan wanda aka ba abu da yawa, za a kuma nemi abu da yawa daga wurinsa. Kuma ga wanda aka ba abu da yawa amana, za a nemi abu mafi yawa daga gareshi.