Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 8

Ayyukan Manzanni 8:1-35

Help us?
Click on verse(s) to share them!
1Bulus ya amince da mutuwarsa. A wannan rana tsanani mai zafi ya fara tasowa akan Iklisiya da take a Urushalima, sai masu bangaskiya duka suka bazu ko ina a cikin garuruwan Yahudiya da Samariya, sai manzannin kadai aka bari.
2Amintattun mutane suka bizne Istifanus suka yi babban makoki game da shi.
3Amma Shawulu ya yi wa Iklisiya mugunta kwarai, ya dinga shiga gida gida yana jawo mutane maza da mata, kuma yana kulle su cikin kurkuku.
4Duk da haka masu bangaskiyar nan da suka warwatsu suka tafi suka dinga yada wa'azin maganar.
5Filibus ya tafi can Samariya ya yi shelar Almasihu.
6Da taron mutane suka ji kuma suka ga alamun da Filibus yake yi, sai suka mai da hankali dukansu domin su ji abinda yake fadi.
7Domin kazaman ruhohi sun fito daga cikin mutane da yawa da suka saurare shi suna kuka da kururuwa; nakasassun mutane dayawa da guragu suka warke.
8Kuma aka yi farin ciki mai girma a birnin.
9Amma akwai wani mutum a cikin birnin da ake kira Siman, wanda tun farko shi masafi ne da kuma dan dabo, yana yi wa mutanen Samariya abubuwan ban mamaki, yayin da yake kiran kansa wani mai muhimmanci.
10Dukan Samariyawa, manya da yara, suna sauraronsa, su kan ce, “Wannan mutum shine ikon Allahn nan wanda ake kira mai girma.”
11Suna sauraron sa, domin ya dade yana yi masu abubuwan mamaki da tsafe-tsafensa.
12Amma da suka yi bangaskiya da wa'azin bisharar da Filibus yake yi game da mulkin Allah da sunan Yesu Almasihu, sai aka yi masu Baftisma dukansu maza da mata.
13Har shima Siman da kansa ya ba da gaskiya. Bayan an yi masa Baftisma ya cigaba da bin Filibus, da ya ga ana nuna alamu da manyan ayyuka, sai ya yi mamaki.
14Da manzannin da ke Urushalima suka ji labarin Samariya ta karbi maganar Allah, sai suka aika masu Bitrus da Yahaya.
15Da suka iso, suka yi masu addu'a, domin su karbi Ruhu Mai Tsarki.
16Domin har wannan lokaci, Ruhu Mai Tsarki bai sauko kan kowannensu ba; an dai yi masu baftisma ne kadai cikin sunan Ubangiji Yesu.
17Sai Bitrus da Yahaya suka dora masu hannuwansu, sai suka karbi Ruhu Mai Tsarki.
18Sa'adda Siman yaga ana bayar da Ruhu Mai Tsarki ta wurin dorawar hannuwan manzanni, ya basu kudi.
19Ya ce, “Ku bani wannan iko, ni ma, don duk wanda na dora wa hannu ya karbi Ruhu Mai Tsarki.”
20Amma Bitrus yace masa, “Azurfarka ta lalace tare da kai, saboda kana tunanin za ka malaki baiwar Ubangiji da kudi.
21Baka da wani rabo a wannan al'amari, domin zuciyarka ba daidai take da Allah ba.
22Saboda haka ka tuba daga wannan muguntarka, ka kuma yi addu'a ga Ubangiji, domin mai yiwuwa ya gafarta maka game da manufar zuciyarka.
23Domin na gane kana cikin bacin rai da kuma cikin daurin zunubi.”
24Siman ya amsa ya ce, “Kayi addu'a ga Ubangiji domina, kada wani daga cikin abubuwan nan da ka fada ya faru da ni.”
25Sa'anda Bitrus da Yahaya suka bada shaida kuma suka fadi maganar Ubangiji, sun koma Urushalima; akan hanya, suka yi wa'azin bishara a kauyukan samariyawa da yawa.
26Yanzu kuwa Mala'ikan Ubangiji ya yi wa Filibus magana cewa, “Tashi ka tafi ta kudu da hanyar da ta yi kasa daga Urushalima zuwa Gaza” (wannan hanyar yana cikin hamada.)
27Ya kuwa tashi ya tafi. Sai ga wani mutum daga Habasha, baba ne mai babban matsayi a karkashin Kandakatu, sarauniyar Habasha. Shine yake mulkin dukan dukiyarta. Ya zo Urushalima domin ya yi ibada.
28Yana komawa zaune cikin karussarsa, kuma yana karanta Littafin annabi Ishaya.
29Ruhun ya ce wa Filibus, “Ka je kusa da karussar nan.”
30Sai Filibus ya gudu ya same shi, kuma ya ji shi yana karanta littafin annabi Ishaya, sai ya ce, “Ka fahimci abin da kake karantawa?”
31Bahabashen ya ce. “Yaya zan iya, idan ba wani ya bishe ni ba?” Ya roki Filibus ya shigo cikin karussar ya zauna tare da shi.
32Wannan kuwa shine nassin da Bahabashen yake karantawa, “An kai shi kamar tunkiya zuwa mayanka; shiru kuma, kamar dan rago a hannun masu sosayarsa, bai bude baki ba.
33Cikin kaskancinsa aka yi masa shari'a da rashin adalci: Wa zai bada tarihin tsararsa? Domin an dauke ransa daga duniya.”
34Sai baban ya tambayi Filibus, ya ce, “Na roke ka, gaya mani, game da wa annabin yake magana? Da kansa, ko kuwa wani mutum dabam?”
35Filibus ya fara magana; akan littafin Ishaya, ya kuwa yi masa wa'azi akan Yesu.

Read Ayyukan Manzanni 8Ayyukan Manzanni 8
Compare Ayyukan Manzanni 8:1-35Ayyukan Manzanni 8:1-35