13Yesu zo ya dauki gurasar ya ba su, haka kuma kifin.
14Wannan shine karo na uku da Yesu ya bayyana ga almajiransa bayan tashinsa daga matattu.
15Da suka karya kumallon, Yesu yace wa Saminu Bitrus, “Bitrus dan Yahaya, kana kaunata fiye da wadannan?” Bitrus yace masa “I ya Ubangiji, ka sani ina kaunarka” Yesu yace masa “Ka ciyar da 'ya'yan tumakina”.
16Ya sake fada masa karo na biyu, “Saminu Dan Yahaya, kana kaunata?” Bitrus Yace masa “I ya Ubangiji, ka sani ina kaunarka”. Yesu yace masa, “Ka lura da Tumakina”.
17Ya sake fada masa, karo na uku, “Bitrus Dan Yahaya, kana kaunata? Sai Bitrus bai ji dadi ba domin Yesu ya fada masa karo na uku, “Kana kaunata” Yace masa, “Ubangiji ka san komai duka, ka sani ina kaunarka.” Yesu yace masa “Ka ciyar da tumaki na.
18Hakika, hakika, Ina gaya maka, lokacin da kake kuruciyarka, kakan yi wa kanka damara, ka tafi inda ka ga dama. amma in ka tsufa, zaka mike hannuwanka wani yayi maka damara, ya kai ka inda baka nufa ba.”
19To Yesu ya fadi haka ne domin ya nuna irin mutuwar da Bitrus zai yi ga daukakar Allah. Bayan ya fadi haka, sai yace wa Bitrus, ka biyo ni.