10Yesu ya ce masu “Ku kawo wandansu daga cikin kifin da kuka kama yanzu”.
11Sai Saminu Bitrus ya hau, ya jawo tarun gaci, cike da manyan kifaye dari da hamsin da uku (153). Amma duk da yawansu, tarun bai tsage ba.
12Yesu yace masu, “Ku zo ku karya kumallo”. Daga cikin almajiran kuwa babu wanda yayi karfin halin tambayarsa “Ko shi wanene?” Domin sunsani Ubangiji ne.
13Yesu zo ya dauki gurasar ya ba su, haka kuma kifin.
14Wannan shine karo na uku da Yesu ya bayyana ga almajiransa bayan tashinsa daga matattu.