Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Romawa - Romawa 1

Romawa 1:6-10

Help us?
Click on verse(s) to share them!
6cikin wadannan al'ummai kwa, ku ma an kiraku ku zama na Yesu Almasihu.
7Wannan wasika ga dukkanku ne da kuke cikin Roma, kaunatattu na Allah, kirayayyun mutane tsarkakakku. Bari alheri ya kasance tare daku, da salama daga Allah Ubanmu, da kuma Ubangiji Yesu Almasihu.
8Abu na farko dai ina yi wa Allah na godiya ta wurin Yesu Almasihu domin ku duka, domin kuwa ana labarta bangaskiyarku ko ina a cikin dukkan duniya.
9Domin kuwa Allah shi ne shaida ta, wanda nake bautawa a cikin ruhuna a cikin bisharar Dansa, yadda a koyaushe na ke ambaton ku.
10A kullum ina roko cikin addu'o'ina domin ta kowanne hali in yi nasarar zuwa gare ku da izinin Allah.

Read Romawa 1Romawa 1
Compare Romawa 1:6-10Romawa 1:6-10