Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 5

Luka 5:4-38

Help us?
Click on verse(s) to share them!
4Da ya gama magana, ya ce wa Siman, “Zakuda jirgin zuwa wuri mai zurfi sa'annan ka zuba tarunka domin kamu.”
5Siman ya amsa ya ce, “Ubangiji, mun yi aiki dukan dare bamu kama komai ba, amma bisa ga maganarka, zan jefa tarun.”
6Da sun yi haka, suka kama kifaye da yawan gaske, har tarunsu suna yagewa.
7Sai suka roki abokan aikinsu da ke a dayan jirgin su zo su taimake su. Suka zo sun cika jiragen biyu da kifaye, har suka fara nutsewa.
8Amma Siman Bitrus, da ya ga haka, ya russuna a gaban Yesu, yana cewa, “Ka rabu da ni Ubangiji, gama ni mai zunubi ne.”
9Domin ya yi mamaki, da dukan wadanda suke tare da shi, sabili da yawan kifaye da suka kama.
10Wannan ya hada da Yakubu da Yahaya 'ya'yan Zabadi abokan aikin Siman. Sai Yesu ya ce wa Siman, “Kada ka ji tsoro, domin daga yanzu, za ka kama mutane.”
11Da sun kawo jiragensu waje kan kasa, suka bar komai suka kuma bi shi.
12Sa'adda yana daya daga cikin biranen, wani mutum dauke da kuturta yana nan wurin. Da ya ga Yesu, ya fadi bisa fuskarsa kasa yana rokansa, yana cewa, “Ubangji, idan ka yarda, za ka iya tsarkake ni.”
13Yesu ya mika hanunsa ya taba shi, yana cewa, “Na yarda. Ka tsarkaka.” Sai nan da nan, kuturtar ta rabu da shi.
14Ya umarce shi kada ya gaya wa kowa, amma ya ce ma sa, “Tafi ka nuna kanka ga firist sa'annan ka mika hadaya domin tsarkakewarka, kamar yadda Musa ya umarta, a matsayin shaida a garesu.”
15Amma labarinsa ya bazu nesa, taron mutane da yawa kuma suka zo wurinsa domin su ji shi, su kuma samu warkarwa daga cututtukansu.
16Amma ya kan janye zuwa wuraren da babu kowa ya yi addu'a.
17Ya zama daya a cikin kwanakin da yake koyarwa, akwai Farisawa da malaman attaura da ke zaune a wurin wandanda suka zo daga kauyukan da suke kewaye da Galili da Yahudiya da kuma birnin Urushalima. Ikon Ubangiji yana tare da shi domin warkarwa.
18A lokacin nan, wasu mutane suka zo dauke da wani mutum shanyayye a kan tabarma, suka kuma nemi yadda za su shigar da shi ciki, su kwantar da shi a gaban Yesu.
19Ba su iya samun hanyar da za su shigar da shi ba saboda taron, sai suka hau saman gidan, suka saukar da shi daga rufin, a kan tabarman sa, zuwa tsakiyar mutanen, dai dai a gaban Yesu.
20Da ya ga bangaskiyarsu, Yesu ya ce, “Maigida, an gafarta zunubanka.”
21Marubuta da Farisawa suka fara sukar wannan, suna cewa, “Wanene wannan da ke sabo? Wa zai iya gafarta zunubi, idan ba Allah kadai ba?”
22Amma da Yesu ya fahimci abin da suke tunani, sai ya amsa ya ce masu, “Don me kuke sukar wannan a zuciyarku?
23Wanne ne ya fi sauki a ce, 'An yafe zunubanka' ko kuwa a ce, 'Tashi ka yi tafiya?”
24Amma domin ku sani cewa Dan Mutum yana da yancin gafarta zunubai a duniya, na ce maka, 'Tashi, dauki tabarmanka, ka tafi gidanka.'”
25Nan take, ya tashi a gabansu ya dauki tabarma da yake kwance; sai ya koma gidansa, yana daukaka Allah.
26Kowa yana ta mamaki kuma suka daukaka Allah. Suna cike da tsoro, suna cewa, “Yau mun ga abubuwan al'ajibi.”
27Bayan wadannan abubuwa sun faru, Yesu ya fito daga can sai ya ga wani mai karban haraji mai suna Lawi yana zama a wurin karban haraji. Ya ce masa, “Ka biyo ni.”
28Sai Lawi ya bar komai, ya tashi, ya bi shi.
29Lawi kuma ya shirya gagarumar liyafa a gidansa, kuma akwai masu karban haraji da yawa a nan, da wasu mutane da ke zama a gaban teburin liyafar suna cin abinci tare da su.
30Amma Farisawa da Marubuta suka fara korafi ga almajiransa, suna cewa, “Don menene kuna ci da sha tare da masu karban haraji da mutane masu zunubi?”
31Yesu ya amsa masu, “Masu lafiya basu bukatar likita, wadanda ke marasa lafiya kadai ke bukatar likita.
32Ban zo domin kiran masu adalci ba, amma na zo ne domin kiran masu zunubi zuwa ga tuba.”
33Sun ce masa, “Almajiran Yahaya sukan yi azumi da addu'a, kuma almajiran Farisawa ma sukan yi haka. Amma almajiranka suna ci suna sha?”
34Yesu ya ce masu, “Akwai wanda zai sa abokan ango su yi azumi, a lokacin da shi ango yana tare da su?
35Amma kwanaki na zuwa wadanda za a dauke ango daga wurinsu, a kwanakin za su yi azumi.”
36Sai Yesu ya sake fada masu wani misali. “Babu wanda zai yage kyalle daga sabuwar tufa, ya kuma yi amfani da ita ya dinka tsohuwar tufa. Idan ya yi hakannan, zai yage sabuwar tufar, kuma kyallen daga sabuwar tufar ba zai dace da kyallen tsohuwar tufar ba.
37Kuma, babu mutum da zai sa sabon ruwan inabi a cikin tsofafin salkuna. Idan ya yi haka, sabon ruwan inabin zai fasa salkunan, kuma ruwan inabin din zai zube, salkunan kuma za su lallace.
38Amma dole ne a sa sabon ruwan inabi a sabobin salkuna.

Read Luka 5Luka 5
Compare Luka 5:4-38Luka 5:4-38