Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 5

Ayyukan Manzanni 5:33-42

Help us?
Click on verse(s) to share them!
33Da yan majalisa suka ji haka sai suka fusata kwarai da gaske, har suka nemi su kashe manzannin.
34Amma wani Bafarise mai suna Gamaliel, malami ne kuma na attaura wanda dukan jama'a suna martabawa, sai ya mike ya ba da umarni cewa a fid da manzannin waje na dan lokaci.
35Sai ya ce masu “Ya ku mutanen Isra'ila, ku lura sosai da a binda kuke niyyar yi wa mutanen nan,
36A kwanakin baya wani ya zo mai suna Tudas ya dauki kansa wani abu, kimanin mutane dari hudu ne suka bishi, amma da aka kashe shi jama'arsa baki daya sai suka watse, ba wanda ya kara jin labarinsu.
37Bayansa kuma, aka yi wani mai suna Yahuza na Galili wanda a kwanakin kidaya, ya zo ya rinjayi mutane da yawa, shima ya lalace, duk wadanda suka bi shi kuwa suka watse.
38Don haka ina gaya maku ku rabu da mutanen nan, domin idan shirinsu ko kuma ayyukansu na mutane ne za su lalace.
39Amnma idan abin nan daga Allah yake baza ku iya lalata su ba; kada ya zama kuna gaba da Allah.” Sai suka rinjayu.
40Da suka kira manzannin ciki suka yi masu duka, sai suka umarce su da cewa kada su sake koyarwa a cikin sunan Yesu, sai suka barsu suka tafi.
41Suka fita daga cikin majalisar, suna murna domin sun cancanta su sha wulakanci saboda sunan.
42Bayan haka kullayomin suna zuwa haikali, suna bi gida gida, suna wa'azi, suna kuma koyarwa ba fasawa cewa Yesu shine Almasihu.

Read Ayyukan Manzanni 5Ayyukan Manzanni 5
Compare Ayyukan Manzanni 5:33-42Ayyukan Manzanni 5:33-42