Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 5:33-42 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 5:33-42 in Litafi Mai-tsarki

33 Da yan majalisa suka ji haka sai suka fusata kwarai da gaske, har suka nemi su kashe manzannin.
34 Amma wani Bafarise mai suna Gamaliel, malami ne kuma na attaura wanda dukan jama'a suna martabawa, sai ya mike ya ba da umarni cewa a fid da manzannin waje na dan lokaci.
35 Sai ya ce masu “Ya ku mutanen Isra'ila, ku lura sosai da a binda kuke niyyar yi wa mutanen nan,
36 A kwanakin baya wani ya zo mai suna Tudas ya dauki kansa wani abu, kimanin mutane dari hudu ne suka bishi, amma da aka kashe shi jama'arsa baki daya sai suka watse, ba wanda ya kara jin labarinsu.
37 Bayansa kuma, aka yi wani mai suna Yahuza na Galili wanda a kwanakin kidaya, ya zo ya rinjayi mutane da yawa, shima ya lalace, duk wadanda suka bi shi kuwa suka watse.
38 Don haka ina gaya maku ku rabu da mutanen nan, domin idan shirinsu ko kuma ayyukansu na mutane ne za su lalace.
39 Amnma idan abin nan daga Allah yake baza ku iya lalata su ba; kada ya zama kuna gaba da Allah.” Sai suka rinjayu.
40 Da suka kira manzannin ciki suka yi masu duka, sai suka umarce su da cewa kada su sake koyarwa a cikin sunan Yesu, sai suka barsu suka tafi.
41 Suka fita daga cikin majalisar, suna murna domin sun cancanta su sha wulakanci saboda sunan.
42 Bayan haka kullayomin suna zuwa haikali, suna bi gida gida, suna wa'azi, suna kuma koyarwa ba fasawa cewa Yesu shine Almasihu.
Ayyukan Manzanni 5 in Litafi Mai-tsarki