Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 22

Ayyukan Manzanni 22:13-26

Help us?
Click on verse(s) to share them!
13Ya zo gare ni ya ce, 'Dan'uwa Shawulu, karbi ganin gari.' A daidai wannan sa'a na gan shi.
14Sa'annan ya ce, 'Allah na kakkaninmu ya zabe ka ka san nufinsa, ka ga Mai Adalcin nan, ka kuma ji muryar da ke fitowa daga bakinsa.
15Gama za ka zama mashaidinsa ga dukan mutane game da abinda ka gani da wanda ka ji.
16A yanzu me ka ke jira? 'Tashi a yi maka baftisma a wanke zunubanka, kana kira bisa sunansa.'
17Bayan da na dawo Urushalima, sa'anda ina addu'a a cikin haikali, sai na karbi wahayi.
18Na gan shi ya ce mani, 'Gaggauta ka bar Urushalima yanzu, domin ba za su yarda da shaidarka game da ni ba.'
19Na ce, 'Ubangiji, su da kansu sun san yadda na sa su a kurkuku na kuma doddoke wadanda suka gaskanta da kai a kowacce masujada.
20A sa'anda a ke zubar da jinin mashaidinka Istifanus, ina nan tsaye ina goyon baya, ina kuma lura da rigunan wadanda suka kashe shi.'
21Amma ya ce mani, 'Tafi, domin zan aike ka can wurin Al'ummai.'
22Mutanen sun bar shi yayi magana har zuwa ga wannan lokacin. Amma sai suka ta da murya suna cewa, 'A kawar da wannan dan taliki daga duniya: don bai kamata ya rayu ba.'
23Sa'anda suke tadda muryarsu, suna jefar da tufafinsu da kuma baza kura a iska,
24babban hafsan ya umarta a kawo Bulus a farfajiyan. Ya umarta da cewa a bincike shi da bulala, domin ya san dalilin da suka ta da ihu gaba da shi haka.
25Bayan da suka daure shi da tsirkiya, Bulus ya ce wa Jarumin da ke kusa da shi, “Ko daidai ne bisa ga doka a yi wa Barome wanda ma sharia ba ta kashe shi ba bulala?”
26Da Jarumin ya ji haka, ya tafi wurin babban hafsan, yana cewa, “Me kake so ka yi? Gama wanan mutumin dan asalin Roma ne.”

Read Ayyukan Manzanni 22Ayyukan Manzanni 22
Compare Ayyukan Manzanni 22:13-26Ayyukan Manzanni 22:13-26