19Bayan da almajiran suka yi tuki na wajen kimanin mil ashirin da biyar ko talatin, sai suka hango Yesu yana tafiya a kan teku ya kuma kusa da jirgin, sai suka firgita.
20Amma ya ce masu, “Ni ne! kada ku firgita.”
21Sa'an nan suka yarda suka karbe shi a cikin jirgin, kuma nan da nan jirgin ya kai gacci.
22Kashe gari, sauran taron da suke tsaye a dayan hayin tekun suka ga cewa babu wani jirgi a wajen sai dayan, Yesu kuma bai shiga ciki da almajiransa ba, amma almajiransa suka tafi su kadai.
23Sai dai, akwai wadansu jirage da suka zo daga Tibariya kusa da wurin da taron suka ci gurasa bayan da Ubangiji ya yi godiya.
24Sa'anda taron suka gane cewa Yesu da almajiransa ba su wurin, su da kansu su ka shiga cikin jiragen suka tafi Kafarnahum neman Yesu.